Yari Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Tawagar Kamfen din Tinubu Ke Ziyartar Sarakuna

Yari Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Tawagar Kamfen din Tinubu Ke Ziyartar Sarakuna

  • Darakta Janar na APC-PCC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce ziyarar sarakuna na neman addu’a da shawarwari ne, ba neman amincewar siyasa ba
  • Tawagar ta ziyarci sarakunan Gwandu, Katsina, Daura da Zariya a wani shiri na tuntuɓar shugabannin gargajiya gabanin zaɓen 2027
  • Manyan shugabannin da suka raka Yari sun haɗa da gwamnonin Kebbi da Zamfara da kuma tsofaffin gwamnoni da wasu jiga-jigan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC-PCC), Sanata Abdulaziz Yari, ya ce ziyarar da su ke kai wa sarakunan gargajiya ba ta da manufar neman amincewar siyasa.

Sanata Yari, tsohon gwamnan Zamfara, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce neman addu’a, albarka da shawarwari masu amfani daga sarakunan gargajiya.

Yari na jagorantar kamfen din Tinubu
Sanata Abdulaziz Yari tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @SenatorAAYari
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci wata tawaga mai ɗauke da manyan shugabannin ƙasa domin ziyartar wasu fitattun masarautun Arewacin Najeriya, kamar yadda aka sanya a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

2027: Shugaban INEC ya sanar da ma'aikatan hukumar abin da ba za su yarda da shi ba

Sarakunan gargajiya 4 da aka ziyarta

A cewar sanarwar da ofishin yaɗa labaran Yari ya fitar, tawagar ta kai gaisuwar ban girma ga Sarkin Gwandu, Mai Martaba Muhammadu Iliyasu Bashar; Sarkin Katsina, Mai Martaba Abdulmumini Kabir Usman; Sarkin Daura, Mai Martaba Umar Faruk Umar; da Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli.

Sanarwar ta ce an tarɓi tawagar cikin girmamawa a fadojin masarautun huɗun, inda sarakunan suka yi addu’o’i tare da roƙon Allah Ya kawo zaman lafiya, haɗin kai da nasara ga tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya.

Tawagar ta tashi ne daga ɓangaren musamman na filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

Manyan shugabannin da suka raka Yari

Daga cikin waɗanda suka raka Yari akwai Gwamnan Kebbi, Dr Nasiru Idris; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare; da tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff.

Sauran sun haɗa da tsohon shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje; tsohon gwamnan Kebbi, Sanata Adamu Aliero; da tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Sani Ahmad Yarima.

Kara karanta wannan

'Yan ISWAP sun sha wuta, sojojin sama sun soya manyan kwamandojinsu

Haka kuma, tawagar ta ƙunshi tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko; tsohon gwamnan Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje; tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shehu Shema; da tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha, tare da wasu shugabanni.

Ya jaddada muhimmancin shawarwarin sarakuna

Yari ya ce jagorancin da sarakunan gargajiya ke bayarwa na da muhimmanci matuƙa ga harkokin siyasar ƙasa.

Sanarwar ta bayyana cewa ziyarar na daga cikin shirin tuntuɓar sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa a faɗin Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.

A cewar sanarwar, kwamitin na ƙoƙarin samar da fahimtar juna da tattara goyon baya yayin da take shirin gudanar da muhimman ayyukan yaƙin neman zaɓe gabanin ranar 16 ga Janairu, 2027, wadda ta bayyana a matsayin muhimmiyar rana a jadawalin zaɓe.

Kwamitin APC-PCC ya sake jaddada girmamawarsa ga masarautun gargajiya, yana mai cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali.

Sanarwar ta ce kwamitin zai ci gaba da tuntuɓar dukkan masu ruwa da tsaki yayin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Sanata Yari ya ziyarci sarakuna
Tawagar Sanata Yari tare da Sarkin Ilorin Hoto: @SenatorAAYari
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya godewa ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) habaici.

Shugaba Bola Tinubu ya gode wa babbar jam'iyyar adawar bisa abin da ya ce ta yi na hana shi yin barci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng