An Kai Maganar Barazana kan Rayuwa Atiku gaban Shugaba Trump
- Tsohon jigon APC, Timi Frank, ya roƙi Donald Trump da ƙasashen duniya su shiga tsakani kan zargin barazana ga Atiku Abubakar
- Frank ya nuna damuwa kan zargin cewa ana iya amfani da hukumomin tsaro da EFCC wajen tsoratarwa ko tsare ɗan takarar shugaban ƙasar na ADC
- Ya jaddada cewa bai kamata a kare ’yan siyasa daga binciken da ya dace ba, amma dole ne a gudanar da bincike ba tare da katsalandan na siyasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar APC, Kwamared Timi Frank, ya roƙi Shugaban Amurka Donald Trump da ƙasashen duniya su shiga tsakani ta hanyar diflomasiyya kan zargin barazana ga rayuwar Atiku Abubakar.
Frank ya kuma nuna damuwa kan zargin yi wa Atiku barazana ta fuskar ’yancin siyasa gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya aika wa Trump da sauran shugabannin ƙasashen duniya ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban 2026.
Frank ya ce akwai rahotannin zargin shirye-shiryen tsoratar da Atiku, kama shi, tsare shi ko kuma hana shi shiga zaɓen mai zuwa yadda ya kamata.
Atiku, wanda ke cikin fitattun ’yan adawa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), na cikin manyan mutanen da ake tattaunawa a kansu yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.
Ya nemi Amurka da ƙungiyoyin duniya su sa baki
Frank ya yi kira ga Amurka, Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Tarayyar Afirka (AU), Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Tarayyar Turai (EU) da Birtaniya da su tattauna da gwamnatin Najeriya.
Ya ce ya kamata ƙasashen da ƙungiyoyin su nemi gwamnatin Najeriya ta bayar da tabbaci mai gamsarwa kan tsaron shugabannin ’yan adawa.

Kara karanta wannan
Yan Najeriya sun maida martani da Tinubu ya ce ba zai iya zuwa kamfe wasu jihohi ba
Frank, wanda jakada ne na ƙungiyar United Liberation Movement for West Papua (ULMWP) a Gabashin Afirka da Gabas ta Tsakiya, ya ce zarge-zargen da suka shafi tsaron Atiku da yiwuwar amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa wa ’yan adawa lamba na buƙatar bincike cikin gaggawa kuma mai zaman kansa.
“Dole ne a gudanar da bincike mai zaman kansa kan waɗannan zarge-zarge cikin gaggawa. Amma saboda muhimmancinsu, bai kamata a yi watsi da su ko a ƙyale su ba har sai an makara wajen hana cutarwa,” in ji shi.
Ya yi gargaɗi kan amfani da hukumomin tsaro
Frank ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na amfani da jami’an tsaro ko hukumomin tabbatar da bin doka wajen hana ’yan takarar adawa shiga zaɓe zai raunana dimokuraɗiyya tare da rage amincewar jama’a ga hukumomin Najeriya.
“Kare ’yan adawa ba wata alfarma ba ce da gwamnati za ta bayar ko ta hana bisa son ranta. Wajibi ne na asali da ke kan kowace ƙasa mai bin tsarin dimokuraɗiyya,” in ji shi.
Ya kuma nuna damuwa kan zargin cewa za a iya amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifukan Tattalin Arziki (EFCC) wajen fara shari’a a kan Atiku a yanayin da zai iya kai ga kama shi da tsare shi na dogon lokaci yayin yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan
Tinubu na tsaka mai wuya, jigon APC ta aika wasika ga shugaban Amurka kan zaben 2027
Sai dai Frank ya bayyana cewa ba ya nufin a keɓe ’yan siyasa daga sahihin bincike. Ya ce abin da ake buƙata shi ne hukumomin tabbatar da bin doka su yi aikinsu cikin ’yanci, ba tare da katsalandan na siyasa ba.
“Abin damuwa ba shi ne a ɗauke Atiku Abubakar a matsayin wanda ya fi ƙarfin doka ba. Abin damuwa shi ne kada a yi amfani da doka wajen tsananta wa mutum saboda siyasa,” in ji shi.
Ya bukaci a gudanar da bincike bisa doka
Frank ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa duk wani bincike da ya shafi ’yan adawa ya dogara da sahihan hujjoji kuma an gudanar da shi bisa ƙa’idojin shari’a.
Ya kuma nuna shakku kan yadda ake amfani da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa ga wasu mutane, amma ba ga wasu ba.
A cewarsa, amincewar jama’a ga hukumomi irin su EFCC ta dogara ne da yadda suke gudanar da bincike cikin adalci, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar wanda ake zargi ba.
Ya jaddada cewa bai kamata a kare wani jami’in gwamnati ko abokin siyasa daga sahihin bincike saboda kusancinsa da fadar shugaban ƙasa ba.
“Idan gwamnati na son ’yan Najeriya su amince da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, dole ne waɗannan hukumomi su nuna cewa adalci ba ya karkata ga wata jam’iyya, kuma ba a zaɓar waɗanda za a bincika bisa son rai,” in ji shi.

Source: Twitter
Hanyar da Atiku zai samu kuri'u
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai taimakawa Atiku Abubakar, Phrank Shaibu, ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 zai kasance mafi sauƙi ga ubangidansa.
Shaibu ya yi hasashen cewa ’yan Najeriya da ke fama da matsin tattalin arziki za su kaɗa wa Atiku ƙuri’a, musamman waɗanda ba su gamsu da yanayin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.
Asali: Legit.ng

