Dan Majalisa Ya Hango Matsala a Dokar Zabe da Za Ta Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
- Ɗan majalisar wakilai, Abdussamad Dasuki, ya nuna damuwa kan wani sashe na Dokar Zaɓe ta 2026 da ya ce zai iya kawo cikas ga sahihanci da amincin zaɓen 2027
- Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar ya nemi a duba kudirin gyaran dokar da kuma gayyatar shugaban hukumar INEC domin ya yi bayani kan shirye-shiryen zaɓen
- Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya yi alƙawarin duba batun tare da ƙoƙarin ganin an sanya ƙudurin a jadawalin muhawara cikin makon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Abdussamad Dasuki (ADC, Sokoto), ya nuna damuwa kan wani sashe na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya ce zai iya kawo cikas ga sahihanci da amincin babban zaɓen 2027.
Dasuki ya gabatar da batun a ƙarƙashin abubuwan da suka shafi gata da haƙƙin ɗan majalisa yayin zaman majalisar, inda ya buƙaci a duba ƙudirin gyaran dokar da ke gaban majalisa tare da tantance shirye-shiryen INEC na gudanar da zaɓen shekara mai zuwa.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar na ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2026.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda har yanzu ba a sanya wani ƙuduri da ke neman gayyatar shugaban INEC domin ya yi wa ’yan majalisa bayani kan shirye-shiryen hukumar ba, duk da cewa an tura shi ga kwamitin da ya dace watanni da suka gabata.
Haka kuma, wani kudirin doka da ke neman gyara Dokar Zaɓe bai samu damar shiga jadawalin muhawara ba.
Ɗan majalisar ya ce kakakin majalisar ya sanya hannu kan ƙudurin da shi da mai tsawatarwa na majalisar suka ɗauki nauyin gabatarwa a ranar 22 ga Yuli, 2026, kafin daga bisani a miƙa shi ga kwamitin kula da dokoki da harkokin kasuwanci na majalisar.
Ya kuma yi nuni da wani kundin bayanan ayyukan majalisa mai kwanan watan 10 ga Yuni, 2026, wanda a cewarsa ya nuna cewa an tattauna kan Kudiri mai lamba 2780 a ranar 21 ga Yuli, yayin da na gaba, mai lamba 2781, wanda shi da shugabancin marasa rinjaye suka ɗauki nauyin gabatarwa, ya ci gaba da kasancewa ba a tattauna da shi ba.

Kara karanta wannan
2027: Shugaban INEC ya sanar da ma'aikatan hukumar abin da ba za su yarda da shi ba
Damuwar Dasuki kan dokar zaɓe
Dasuki ya ce an gabatar da kudirin ne domin magance matsalolin da ake ganin za su iya shafar sahihancin tsarin zaɓe, musamman wani sashe na 63 na Dokar Zaɓe ta 2026.
A cewarsa, wannan sashe na iya ba jami’an zaɓe damar karɓar takardun ƙuri’a waɗanda ba su da alamomin tsaro da INEC ta tanada.
“Yau, yayin da muke magana, Dokar Zaɓe ta 2026 tana da wasu matsaloli da suka shafi sahihanci, kuma wannan shi ne abin da muke son magancewa,” in ji shi.
Ya kwatanta gibin da yake zargin akwai a dokar da halin da ake ciki inda banki zai karɓi jabun kuɗi saboda kawai an haɗa su cikin damin kuɗi.
Ya nemi a tantance shirye-shiryen INEC
Mataimakin shugaban marasa rinjayen ya kuma buƙaci majalisar ta gayyaci shugaban INEC domin ya yi bayani kan matakin shirye-shiryen hukumar na gudanar da babban zaɓen 2027.
Ya danganta buƙatar tasa da damuwar da ake da ita kan samar da kuɗaɗen gudanar da zaɓe da kuma matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
Dasuki ya yi gargaɗin cewa bai kamata majalisar ta jira sai gab da zaɓe kafin ta tantance shirye-shiryen hukumar ba. Ya ce kundin tsarin mulki ya ba Majalisar Tarayya ikon neman bayani daga INEC kan irin shirye-shiryen da take yi.
“Ba ma son mu jira sai jajibirin zaɓe kafin mu san abin da INEC za ta yi. Mu ne kaɗai kundin tsarin mulki ya ba ikon tambayar INEC yadda ta shirya,” in ji shi.
Ya ƙara bayyana damuwarsa kan kuɗaɗen da hukumar za ta samu, yana mai cewa ya kamata ’yan majalisa su tabbatar ko tana da isassun kuɗaɗen gudanar da zaɓen.
Dasuki ya roƙi kakakin majalisar da ya tabbatar an sanya kudirin gyaran dokar da ƙudurin gayyatar shugaban INEC a jadawalin muhawara. Ya nuna cewa an riga an kai ga Kudiri mai lamba 2792 a jerin waɗanda za a tattauna, alhali nasa kudirin yana da lamba 2781.
Shugaban majalisa ya yi alƙawarin duba batun
Da yake mayar da martani, kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya tabbatar wa Dasuki cewa zai duba batun tare da bincika yiwuwar sanya ƙudurin a jadawalin muhawara cikin makon.
Sai dai Abbas ya tambayi dalilin da ya sa ɗan majalisar ya zaɓi gabatar da batun a gaban dukkan ’yan majalisa maimakon ya kawo shi a taron shugabancin majalisar da aka gudanar kwanakin baya, inda ya ce da an samu damar tattauna shi.
Duk da haka, kakakin majalisar ya yi watsi da zargin cewa akwai wata muguwar manufa a bayan jinkirin, yana mai tabbatar wa Dasuki cewa za a duba batun.

Source: Twitter
An gargadi ma'aikatan INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya gargaɗi ma’aikatan hukumar.
Farfesa Amupitan ya gargade su kan shiga siyasar jam’iyya, inda ya buƙace su da su kasance masu tsaka-tsaki da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
Asali: Legit.ng


