Anyanwu Na Nan Daram a Matsayinsa Na Sakataren PDP Ta Ƙasa, In Ji NWC

Anyanwu Na Nan Daram a Matsayinsa Na Sakataren PDP Ta Ƙasa, In Ji NWC

  • Jam'iyyar PDP ta ƙasa ta musanta ikirarin wata ƙungiyar cewa NWC ya kori sakataren jam'iyya na ƙasa, Samuel Anyanwu
  • Ta ce Anyanwu na nan daram a matsayinsa na sakataren PDP na ƙasa kuma shi ne ɗan takarar gwamnan Imo a zaɓen watan Nuwamba
  • Kakakin PDP na ƙasa, Ologunagba, ya karyata batun, inda ya ce wasu ne suka kirƙira don raba kan jam'iyyar

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ta ƙasa (NWC) ya bayyana cewa Sanata Samuel Anyanwu, na nan a matsayin Sakataren jam'iyyar na ƙasa.

NWC ya yi bayanin cewa duk da Sanata Anyanwu shi ne ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a zaɓen jihar Imo mai zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, yana nan a kujerar Sakatare.

Sakataren PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu.
Dan takarar gwamnan PDP a jihar Imo, Samuel Anyanwu Hoto: OfficialPDP
Asali: Facebook

Jam’iyyar ta yi wannan karin haske ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Yarda Ya Yi Aiki da Tinubu

Ologunagba ya ce an ja hankalin jam’iyyar PDP kan wata sanarwa da wata kungiya ta fitar mai iƙirarin cewa NWC ya kori Anyanwu daga mukaminsa na sakataren jam'iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan wanda PDP ta wallafa a shafinta na manhajar X, Mista Ologunagba ya ce:

“Kwamitin NWC na tabbatar da cewa ikirarin da kungiyar ta yi gaba daya karya ce, domin babu lokacin da NWC ya yi tunanin sauke sakatare na kasa, Anyanwu daga mukaminsa."
"Saboda haka NWC ya yi Allah wadai da abinda wannan ƙungiya ta aikata wanda ya nuna a fili cewa wasu gurɓatattu ne ke kokarin raba kawunan jam'iyyar PDP."
“NWC tana mai gargadin cewa duk yadda mutum ko kungiya ke ji game da wani lamari, wanda ya kai ga ƙage, karya da ikirarin yanke hukunci ba daga NWC ba, mun yi Allah wadai."

Kara karanta wannan

An Bayyana Ainihin Dalilin da Ya Sanya Wike Ya Gana da Bukola Saraki

Ya roƙi ‘yan Najeriya musamman magoya bayan PDP a Imo su yi watsi da ikirarin na karya domin Anyanwu shi ne sakataren PDP na kasa kuma dan takara a zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba.

"Ba Mu Dakatar da Shirin Tsige Mataimakin Gwamna Ba" Majalisar Ondo

A wani rahoton kuma Kujerar mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, na kan siraɗi mai wahala har yanzu dangane da batun tsige shi.

Majalisar dokokin jihar ta musanta rahotanni da ke yawo cewa ta dakatar da shirin sauke mataimakin gwamna daga kan kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel