Hajjin Bana
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kammala jigilar Alhazan Najeriya da suka je sauke farali a kasa mai tsarki. Alhazan Kwara suka hau jirgin karshe daga Saudiyya.
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce a yau Talata jirgin farko dauke da wadanda su ka kammala aikin hajjin bana kimanin 554 za su iso gid.
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kebbi ta tabbatar da rasuwar Hajiya Maryamu daga ƙaramar hukumar Maiyama, ta rasu ne a asibitin Sarki Abdul'aziz da ke Makkah.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wata Hajiya 'yar jihar Neja a kasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024. Ta rasu ne a birnin Makkah.
Wasu Alhazai mutum biyu na jihar Kebbi sun riga mu gidan gaskiya. Gwamnatin jihar ta tabbatar da rasuwarsu inda ta mika sakon ta'aziyya bisa wannan rashi.
Hukumar NAHCON ta jinjinawa mahajjaci mai suna Muhammad Na'Allah daga yankin Gummi a jihar Zamfara da ya mayar da kudin tsintuwa da suka kai €1,750.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bukaci majalisar tarayya da ta binciki tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta ba hukumar NAHCON domin hajjin bana.
Kungiyar 'yan jarida ta IHR ta jinjinawa hukumar jin dadin alhazai a jihar Kaduna bayan dawowa mahajjata kudi kimanin $50 saboda sauki da aka samu kan hadaya.
Jirgin farko da ya kwaso alhazan Najeriya daga Saudiya ya Iso gida. Kashi na farko na alhazai 410 daga jihar Kebbi da suka yi aikin Hajjin bana sun dawo gida.
Hajjin Bana
Samu kari