Hajjin Bana
NAHCON ta amince da Naira miliyan 8.7 a matsayin kudin aikin Hajjin 2025 ga maniyyatan Kudu, sai Naira miliyan 8.3 ga 'yan Arewa maso Gabas. Ta yi karin bayani.
NAHCON ta sanar da cewa gwamnati ta zabi jirage 4 don jigilar alhazai a aikin Hajjin 2025. Haka zalika, hukumar ta cimma yarjejeniya da kasar Saudiyya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya roki alfarma wajen shugaba Bola Ahmed Tinubu domin rage kudin aikin hajjin 2025 saboda matsin tattalin arziki da ake fuskanta
Hukumar Kula da Alhazan Kaduna ta fara biyan N61,080 ga Alhazai 6,239 da suka yi aikin Hajj a 2023, bayan matsalar wutar lantarki da ta faru a Muna.
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta shirya daina amfani da Dala wajen biyan kudaden abubuwan da suka shafi aikin Hajji. Ta ce hakan zai rage tsadar aikin Hajji.
Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa watau NAHCON ta maidawa kowane maniyyaci N60,080 a jihar Kebbi saboda wani hakkinsu da ba a biya masu ba a 2023.
Hukumar alhazai ta jihar Kano ta mayarwa kowane alhaji alhaji sama da N61,000 sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a Minna lokacin aikin hajjin shekarar 2023.
Gwamnatin Kano ta na zuba ido don a fara sayen kujerun aikin hajjin bana. Hukumar jin dadin alhazai ta koka kan karancin sayen kujerun, yayin da shiri ke kankama.
Hukumar alhazai a jihar Jigawa za ta mayar da makudan kudi har N95m ga mahajjata da suka gudanar da aikin hajjin shekara 2023 da aka gudanar a Saudiyya.
Hajjin Bana
Samu kari