Wahalar man fetur a Najeriya
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa za a samu saukin farashin man fetur a Najeriya idan darajar Naira ta karu> Ya ce zai kara gidajen man fetur zuwa 2,000.
Da yiwuwar ƴan Najeriya su tsinci kansu a matsalar ƙarancin mai da karuwar ra ayyukan yi sakamakon haramta amfani da tankoki masu cin lita 60,000 yau Asabar.
NMDPRA ta rufe gidajen mai 5 a Katsina saboda matse lita da rashin tsaro. NMDPRA ta zayyana sunayen gidajen da aka rufe suka hada da A A Rano, Ashafa da wasu uku.
Masu shigo da mai daga ketare sun ce kasuwancinsu na cikin matsala bayan matatar Ɗangote ta sake rage farashin litar man fetur, sun ce za su iya yin asara.
Kamfanin Dangote Refinery ya sake rage farashin fetur daga ₦890 zuwa ₦825 kowace lita inda aka tabbatar da cewa a Lagos za a siyar da lita kan ₦860.
Direbobin tankunan mai sun dakatar da ɗaukar kaya a Lagos, lamarin da ke barazana ga wadatuwar man fetur da dizal, tare da haddasa fargabar katsewar sadarwa.
Kungiyar direbobin manyan motoci ta bayyana cewa umarnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar a kan dakon mai zai rage shigo da fetur Arewa.
Yayin da ake kokawa kan yawan haduran tankokin mai da ake samu, Hukumar NMDPRA ta haramta amfani da tankokin mai masu daukar lita 60,000 a hanyoyin Najeriya.
Bayan yada wani bidiyo a Najeriya, Kamfanin NNPCL ya karyata zargin cewa man fetur dinsa bai da inganci, yana mai cewa binciken da aka yi ba shi da tushe.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari