Da Gaske Man NNPCL Ya Fi Saurin Konewa kan na Dangote? Kamfani Ya Kare Zargi
- NNPC ya karyata zargin cewa fetur dinsa bai da inganci, yana cewa wani binciken da aka yi ba shi da tushe kuma ba a tabbatar ba
- A cikin wani bidiyon, an nuna man Dangote yana da inganci fiye da na shi, amma NNPC ya ce sam wannan ikirari ba gaskiya ba ne
- NNPC ya gargadi masu yada ƙarya da nufin bata masa suna, yana cewa zai ɗauki matakin doka kan masu yada bayanan ƙarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kamfanin mai na (NNPC) ya karyata ikirarin da aka yi a bidiyon da ya bazu cewa man fetur dinsa bai da inganci.
Kamfanin ya yi fatali da labarin inda ya yi gargadi ga al'umma su bar yada bayanan karya.

Asali: Facebook
Kamfanin NNPCL ya ƙaryata rashin ingancin mansa

Kara karanta wannan
Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook
Jami'in hulda da jama'a na NNPC, Olufemi Soneye ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olufemi ya karyata bidiyon da aka yada inda ake cewa man NNPC bai kai na Dangote inganci ba.
A bidiyon, wani mutum ya yi amfani da janareta guda biyu don gwada tsawon amfani tsakanin man Dangote da na NNPC, yana cewa na MRS yafi inganci.
NNPC ya bayyana wannan ikirari a matsayin maras tushe da makama, yana cewa binciken da aka yi ba a tabbatar da shi ba kuma ba shi da sahihanci.
“NNPC na ƙaryata wannan ikirari na ɓatanci da ya nuna cewa man NNPC bai da inganci, wannan ikirari ba shi da tushe kuma ƙarya ne."
- Olufemi Soneye
NNPC ya ce man fetur ɗinsa an tsara shi yadda zai ba da inganci, ɗorewa da kuma kare muhalli ga masu amfani da shi.
NNPCL ya fadi yadda yake samun fetur a Lagos
Kamfanin ya ƙara da cewa kaso mai yawa na man da ake sayarwa a gidajen man NNPC a Legas, inda aka yi bidiyon, daga matatar Dangote ne.
“Matatar Dangote tana biye da ƙa’idojin masana’antu masu tsauri, tana tabbatar da ingancin man da ake sayarwa ga masu amfani da shi.
“Wannan bidiyon na ƙarya wani yunƙuri ne na masu son bata wa NNPC suna don haka ba zai lamunci irin wannan ƙarya ba."
- Olufemi Soneye
Ya ƙara da cewa daga yanzu, NNPC zai ɗauki matakin doka kan duk wanda ke yaɗa ƙarya kan kamfanin.
NNPC ya ce za ta ci gaba da tabbatar da wadatar man fetur mai inganci da araha ga ‘yan Najeriya tare da bin ƙa’idojin duniya.
Legit Hausa ta tattauna da mai siyar da mai
Wani dan kasuwar man fetur, Hussaini Muhammad ya yi tsokaci kan zargin da ake yi.
Ya ce mafi yawan masu ababan hawa suna yawan korafi kan man fetur na NNPCL ko kuma wasu gidajen mai da suka camfa.
"A gaskiya wani lokaci za ka ji masu ababan hawa na korafi amma ba zan iya gane hanyoyin bambance ingancin mai ba ko akasin haka ba."
-Cewar Hussaini
Sai dai ya ce wasu kuma sun fi raja'a zuwa gidajen mai NNPCL ba don komai ba sai saboda sauki da ake samu ba tare da la'akari da wani abu ba.
NNPCL ya ƙara sauki farashin man fetur
Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa kamfanin NNPCL na kasa ya rage farashin litar man fetur a wasu gidajen mai.
Bincike ya nuna a wasu gidajen man NNPCL da ke birnin Abuja, farashin ya kasance a yadda yake ba tare da an yi sauyi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng