Yaki da ta'addanci a Najeriya
UNICEF ta ce Najeriya ta yi asarar dala biliyan 10 saboda rikicin Boko Haram, yayin da aka ƙaddamar da shirin dawo da yara cikin al’umma a Borno.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta karyata zargin cewa ana kisan Kiristoci, tana cewa hare-haren ‘yan ta’adda bai shafi addini ba kwata-kwata.
Mazauna Banki a Borno sun bayyana yadda Baturen 'yan sandan yankin ya tattara kawunan jama'a da 'yan sanda a lokacin da mayakan Boko Haram su ka kai hari.
Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta kama mutum daya cikin wadanda ake zargi da fille kan wata tsohuwa yar shekara 69 a jihar Anambra, ana kokarin kama sauran.
Tsoro da firgici sun karade Rafi da Wushishi a Neja bayan 'yan ta’adda sun bayyana da makamai, suna harbe-harbe yayin da jama’a ke tserewa daga gidajensu.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira da babbar murya ga mutanen da ke rayuwa a kan iyaka. Ya bukaci ka da su bari 'yan ta'adda su kore su.
Mazauna Kebbe, Sokoto, sun koka kan hare-haren ‘yan bindiga da suka kashe mutane, suka sace sama da 30, suka lalata garuruwa 17, yayin da gwamnati ta yi martani.
Sarkin Kirawa ya tsere zuwa Kamaru bayan Boko Haram sun kai hari suka ƙone fadarsa, suka kashe mutane biyu, yayin da dubban jama’a suka gudu daga Gwoza.
Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya fayyace gaskiya bayan juya masa magana kan alakanta kungiyar Boko Haram da marigayi Muhammadu Buhari.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari