Nade-naden gwamnati
Baya ga irinsu Nasir El-Rufai, ysohon Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya na cikin jerin Ministocin Bola Ahmed Tinubu da aka karanto a majalisar dattawa a yau.
A dokar kasa, shugaban kasa da gwamnoni su na da wa'adin kwanaki 60 ne kacal don fitar da jerin sunayen ministoci da kwamishinoni bayan rantsar da su a mulki.
Majiyoyi sun bayyana cewa an saka sunan Muhammad Ali Pate, tsohon karamin ministan lafiya a gwamnatin Goodluck Jonathan cikin jerin ministocin Shugaba Tinubu.
Tsohon ministan Buhari, Lai Mohammed ya samu matsayi inda aka nada shi mai ba wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a bangaren yawon bude ido shawara.
Rahotanni sun kawo cewa tsohon ministan babban birnin tarayya, Mallam Nasir El-Rufai na iya zama ministan wutar lantarki a gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu.
Seyi Tinubu dan farin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ya na da tabbacin shugaban ba zai ba wa 'yan kasar kunya ba, ya gode musu da irin hadin kai da suke ba su.
Majiyoyi sun bayyana wanda shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake shirin gabatarwa majalisa domin ya zama Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a.
Da alama Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da shawarar Gwamnonin APC wajen rabon mukamai. Gwamnan Jigawa ya ce sun tofa albarka a jerin Ministocin da za a nada.
A matsayinsa na Mai ba shugaban majalisa shawara, Jackson Akpabio ya ce za a san wadanda za su iya zama Ministoci, ya nuna ya ci karo da sunayen da za a gani.
Nade-naden gwamnati
Samu kari