Ministan Buhari, Lai Mohammed Ya Sake Samun Sabon Mukami Mai Muhimmanci

Ministan Buhari, Lai Mohammed Ya Sake Samun Sabon Mukami Mai Muhimmanci

  • Tsohon ministan yada labarai a Najeriya, Lai Mohammed ya samu babban matsayi a Majalisar Dinkin Duniya
  • An nada Lai a matsayin mai ba da shawara kan yawon bude ido na babban sakatare, Zurab Pololikashvili
  • Lai shi ne dan Najeriya na farko da ya fara rike wannan matsayi a tarihi, ya yi godiya da irin wannan dama da aka ba shi

FCT, Abuja - Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a bangaren yawon bude ido, Zurab Pololikashvili ya nada tsohon ministan Buhari, Lai Mohammed a matsayin mai ba shi shawara.

An sanar da nadin nasa ne a cikin wata sanarwa yayin bikin majalisar da ake yi na 66 a Mauritius, TheCable ta tattaro.

Tsohon ministan Buhari, Lai ya samu matsayi matsayi mai muhimmanci
Tsohon Ministan Buhari, Lai Mohammed Ya Samu Babban Matsayi A Majalisar Dinkin Duniya. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Lai ya samu matsayi a Majalisar Dinkin Duniya

Lai Mohammed ya kasance tsohon ministan yada labarai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

"Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jawowa Abdullahi Adamu Rasa Shugabacin APC"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana sa ran tsohon ministan zai taimawa Zurab wurin inganta yawon bude ido a Nahiyar Afirka, cewar Vanguard.

Lai ya bayyana jin dadinsa akan wannan mukami inda ya ce shi ne dan Najeriya na farko da ya fara rike wannan matsayi.

Lai ya bayyana jin dadinsa da kuma godiya

A cewarsa:

"Na tsaya a gaban ku cikin jin dadi saboda kalamanku na yarda da kuma aminci.
"Ina matukar godiya yadda babban sakatare Mista Zurab ya samu kwarin gwuiwa a kai na."

Ya kara da cewa kamar yadda Daily Nigerian ta tattaro:

"Cikin kan-kan da kai na karbi wannan mukami na mai ba da shawara a bangaren yawon bude ido na babban sakataren wannan kungiya mai daraja.
"Na ji dadi da na kasance dan Najeriya na farko da ya rike wannan matsayi, kasar ta ci gaba ta fannin yawon bude ido da masana'antu da al'adu da fasaha da sauransu."

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Za a Ƙara Cin Wahala, Masani Ya Yi Hasashen Shekarar Samun Sauƙi

Kwanaki Kadan Da Barin Kujerarsa, Ministan Buhari Ya Samu Mukami Babba

A wani labarin, tsohon ministan Buhari ya sake samun babban matsayi kwanaki kadan bayan barin mulki.

Tsohon ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya samu matsayin a wani kamfani mai suna Ballard Partners.

Bayan shafe shekaru a Turai da Amurka, wannan kamfani na Duniya ya shigo nahiyar Afrika kuma zai bude ofishinsa a manyan biranen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel