Aikin Gwamnatin Najeriya
Kamar yadda Hukumar RMFAC ta yanka, a albashi akwai, Minista ya na samun N650,135.99 a wata. Alawus da gwamnatin tarayya ta ke biyan Minista sun kai biliyoyi.
Ministan ayyuka na tarayya, David Umahi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa zata gina gada a titim Abuja zuwa Lokoja domin kawo karshen wahalhalun ambaliyar ruwa.
Samuel Ortom ya na cikin ‘Yan tawagar G5 da su ka yaki PDP a zaben 2023, ya ce Nyesom Wike zai kawowa birnin Abuja cigaba, ya kuma yabi cancantar Joseph Utsev.
Lateef Fagbemi ya na cikin wadanda aka fara rantsarwa a kujerar minista, shi ya zama babban lauyan gwamnatin tarayya, za ku ji aikin da ke gaban dukkaninsu.
An gano ashe Naira biliyan 5 na rage radadin cire tallafin mai da fg za ta raba wa jihohi bashi ne. Kudin Tallafin da Za a ba Jihohin bashi ne Ba Kyautar ba.
Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya koka game da halin tattalin arzikin da al’umma ta ke ciki. Dr. Gumi ya ce wasu ne ke zuga Bola Tinubu wajen gallazawa jama’a.
Ana da labari Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da ministocin gwamnatinsa a ranar Litinin, mun kawo yadda aka canza fasalin ma’aikatun kasar nan.
Bola Tinubu ya dauki aro a wajen tsohon shugaban kasar, bai bada babbar kujerar Ministan fetur ba. A lokacin Muhammadu Buhari, shi ne babban Minista na mai.
Gwamnatin tarayya ta karkashin BPE, za tayi gwanjon kayan gwamnati da nufin samun kudi. Dama Atiku Abubakar ya na da ra’ayin a cefanar da irinsu kamfanin NNPC.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari