Buhari Ya Roki Majalisa Ta Bada Damar Ya Karbo Aron $800m a Karshen Mulkinsa

Buhari Ya Roki Majalisa Ta Bada Damar Ya Karbo Aron $800m a Karshen Mulkinsa

  • Muhammadu Buhari ya rubuta wasika zuwa majalisar dattawa da nufin ya karbo bashin kudi
  • Shugaban kasar Najeriya yana so Sanatoci su sake amince masa, wannan karo ya karbo $800m
  • Za a yi amfani da kudin da za a karba daga bankin Duniya domin taimakawa mutum miliyan 50

Abuja - Muhammadu Buhari wanda kwanaki 19 suka rage mai a mulkin Najeriya, ya aika takarda zuwa majalisa domin ya karbo bashin kudi.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa wasikar da shugaban na Najeriya ya rubutawa majalisar dattawa za ta ba shi damararo $800m.

Mai girma Muhammadu Buhari yana so ya ci sabon bashin kudin ne daga babban bankin Duniya.

Buhari
Muhammadu Buhari a ofis Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Me za ayi da kudin?

Dalliin karbo bashin daga kasar waje shi ne a rage radadin da al’ummar Najeriya za su shiga idan gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Ankarar da Tinubu Tun Yanzu, Ya Sake Bada Shawarar Janye Tallafin Fetur

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoto ya ce ana so ayi amfani da kudin a taimakawa rayuwar mutane miliyan 50 marasa galihu, ana sa ran kudin ya taba gidaje miliyan goma.

A baya, Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce Gwamnatin tarayya za ta daina biyan tallafin fetur a Yuni.

Zuwa yanzu ba mu san matsayar da majalisar dattawa ta dauka game da wannan bukata ba.

Bisa al’ada, sai kwamitin da yake lura da harkokin bashi ya yi zama a kan takardar shugaban kasar, daga nan majalisar dattawa ta dauki mataki.

N360bn ga mutane miliyan 50

Da Legit.ng Hausa tayi lissafi a farashin canjin kudi a yau, adadin abin da gwamnatin Najeriya ta ke neman karbowa ya zarce Naira biliyan 360.

A 2015, bashin da ake bin Najeriya a kasar waje bai wuce $10.32b ba. Kamar yadda Shehu Sani ya fada, APC tana hawa mulki ya karu da 114%.

Kara karanta wannan

Buhari: Abin da Ya Sa Na Ki Fitowa Karara In Goyi Bayan Magajina a Zaben Gwanin APC

Ganin yadda bashin yake hawa ne majalisa ta takwas ta ki amincewa da wasu bukatun shugaban kasar, ta hana shi ycin bashi daga ketare.

Jonathan ya jinjinawa NASENI

A rahoton da aka fitar a ranar Laraba, an ji yadda mutane 100 za su amfana da horaswar da gwamnatin tarayya za tayi a Otuoke a jihar Bayelsa.

Tsohon Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan wanda ya fito daga yankin, ya ji dadin alherin da aka kawo masu ta karkashin hukumar NASENI.

Asali: Legit.ng

Online view pixel