Gwamnoni Sun Fadakar da Najeriya a Kan Hadarin da Ake Dosa a Gwamnatin APC

Gwamnoni Sun Fadakar da Najeriya a Kan Hadarin da Ake Dosa a Gwamnatin APC

  • Akwai Gwamnonin jihohi da suke ganin bashin da ake bin Gwamnatin Najeriya ya fara yin yawa
  • Wasu Gwamnoni sun tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin a wajen zaman da NGF ta shirya masu
  • Har zababbun Gwamnoni masu jiran gado sun tsorata da yadda Gwamnatoci suke yawan cin bashi

Abuja - Wasu Gwamnonin jihohi sun fito karara sun nuna damuwarsu a kan yadda bashin da ake bin gwamnatin Najeriya ya tashi a ‘yan shekaru nan.

Leadership ta ce Gwamnonin kasar su na tsoron cewa idan ba a dauki matakan da suka kamata ba, bashin zai zo ya kawowa gwamnatin tarayya matsala.

Gwamnonin sun yi jawabi ne a wajen wani zama na musamman da kungiyar NGF ta shiryawa zababbun Gwamonin jihohi, an yi taron ne a fadar Aso Rock.

Gwamnoni
Zaman da aka shiryawa Gwamnoni Hoto: @sanusi.dawakintofa
Asali: Facebook

Bala Mohammed ya koka

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Zugo Hukumar EFCC Ta Binciki Duka Mukarraban Gwamnatin Buhari

Gwamna Bala Mohammed ya nuna takaicinsa a kan yadda 95% na duka abin da Najeriya ta ke samu a matsayin kudin-shiga su ke karewa a biyan bashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Bala Mohammed ya ce idan ba ayi hattara ba, tattalin arzikin kasar nan zai ruguje.

Gwamnan na jihar Bauchi ya yi mamakin yadda har yanzu Bankin Duniya bai ja-kunnen gwamnatin Najeriya a kan yawon bashin da suke karbowa ba.

An rahoto cewa Bala ya nuna ya kamata zuwa yanzu a ce Bankin Duniya ya fadawa Najeriya ba za ta yiwu ta cigaba da rika cin bashi babu kai-babu gindi ba.

Mutfwang da Radda sun yi magana

Zababben Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang ya na tare da Gwamnan jihar Bauchi, ya nuna ana bukatar dukiyar da za a biya bashin da yake wuyan gwamnati.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Cikas 1 da Ya Hana Ni Maganin Barayin Gwamnati a Mulkina

Gwamnan mai jiran-gado ya yi bayanin muhimmancin gwamnatocin jihohi da na tarayya su kirkiro dabarun da za su taimaka wajen raba kan su da bashi.

Bayan Caleb Mutfwang, an ji Dikko Umar Radda ya na cewa zai duba bashin da ake bin Jihar Katsina da zarar ya dare kan kujerar Gwamna nan da kwanaki.

Dikko Radda ya ce zai canza fasalin bashin kudin da ake bin Gwamnatin jihar Katsina domin ya iya sauke nauyin al’ummar jiharsa da zai shugabanta.

Rikici a kan rabon $15m

Rahoto ya zo ana zargin an ba Femi Gbajabiamilla Dalolin miliyoyi da ya amince da takardar Gwamnatin Tarayya na canza salon bashin da aka ci daga CBN.

Zargin da ake yi shi ne, da ya karbi $15m, Shugaban majalisar ya soke $11m, sai ake zargin ya aikawa ‘Yan majalisa $10, 000 wanda hakan ne ya jawo rigima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel