Aikin Gwamnatin Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kuduri aniyar aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye da ya nemi gwamnati ta hade wasu hukumomi waje daya tare da rushe wasu.
Kungiyar kwadago ta yi zargin cewa ta gano wani shiri da aka yi na kai hare-hare kan 'yan kungiyarta da za su gudanar da zanga-zangar lumana a fadin kasar.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta yi wa jama’a karin haske game da ayyukan ‘yan damfara da ke yaudarar masu neman aiki a kasar.
Bola Tinubu ya cigaba da yin ruwan nade-nade a mulki. Tinubu ya amince da nadin shugabanni da-dama da za su kula da hukumomi da kamfanoni a ma’aikatar sadarwa.
Gbenga Alade aka zaba ya zama shugaban AMCON mai kula da kadarorin Najeriya. Shugaba Bola Tinubu ya katse wa’adin Malam Ahmed Kuru wanda Muhammadu Buhari ya nada.
Gwamnatin Bola Tinubu za ta rika yin rabon kudi duk wata ga wadanda suke cikin fatara. Wale Edun ya ce an shirya dawo da tsarin inganta rayuwar marasa galihu.
Tun kwanakin baya gwamnatin Bola Tinubu ta ce za a fito da buhunan hatsi a raba. An shafe makonni 2 da yin alkawarin rabon hatsi, ‘yan Najeriya suna jiran tsammani.
A bara Bola Tinubu ya aiko takarda zuwa ga majalisar dattawan, ya nemi a tabbatar da nadin da ya yi. Yanzu an amince da mutane 17, an yi watsi da wasu biyu.
Shugaban majalisar dattawa ya ce kowace jiha ta samu N30bn saboda a samar da abinci. Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya ce ta hannun FIRS aka fitar da kudin.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari