Za a Datse Masu Albashi: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Bayani Bayan Tantance Ma’aikata

Za a Datse Masu Albashi: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Bayani Bayan Tantance Ma’aikata

  • Gwamnatin Najeriya ta tantance ma’aikatanta da ke karkashin manhajar IPPIS domin bankado rin rashin gaskiya da ake tafkawa
  • Idan an kammala wannan aiki, akwai ma’aikatan da za a daina biyansu albashi kamar yadda sanarwa ta fito daga babban birnin Abuja
  • Za a tsaida albashin duk wani wanda ba a samu cikakken bayaninsa ba a yunkurin ganin an rage kudin da ake kashewa a albashi

Abuja - Gwamnatin tarayya ta na barazanar korar duk wani ma’aikaci da ba a iya tantace bayanansa a manhajar albashi ta IPPIS ba.

Darektan sadarwa na ofishin Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mohammed Ahmed ya sanar da haka, Tribune ta kawo rahoton.

A jawabin da ya fitar a ranar Laraba, Ahmed ya yi gargadi cewa sun bada makonni biyu a tantance ma’aikatan da za a yi wa karin albashi.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Ba Tinubu Shawarwarin Da Za Su Taimaka Wajen Dawo da Darajar Naira

Shugaban kasa
Ana tantance ma'aikata kafin a kara albashi Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Za a tsaida albashin wasu ma'aikatan

Duk wanda ba a iya tantacewa ba, za a cire sunansa daga jeringiyar wadanda za su rika karbar albashin wata daga gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce wa’adin zai kare bayan 27 ga Oktoba, daga nan sai a dakatar da albashi.

Gwamnati ta tantance ma'aikata a Abuja

Darektan ya ce da farko wa’adin ya wuce, amma da wasu ma’aikata su ka nemi alfarma, sai aka bude shafin na tsawon kwanaki goma.

Ahmed ya ce an bukaci irin wadannan ma’aikata su zo Abuja domin gwamnati ta karar da kudin da aka ware domin aikin ta yanar gizo.

Dalilin bincike a kan ma'aikata - Gwamnati

Vanguard ta rahoto shi ya na mai cewa ana amfani da manhajar IPPIS ne domin rage kashe kudi ta hanyar gano ma’aikatan bogi a gwamnati.

Kara karanta wannan

Uba Ya Shiryawa Diyarsa Kasaitaccen Biki Na Dawowarta Gida Bayan Mutuwar Aurenta, Bidiyon Ya Yadu

"Wadanda wannan abin ya shafa su ne su ka jawo kansu domin ba su bi umarnin gwamnati ba.
Za a kammala aikin tantancewar a karshen wannan aiki kuma duk wanda ba a samu bayanansa ba zai fita daga aljihun gwamnati."

- Mohammed Ahmed

Albashi bai isa ayi cefane

Cire tallafin man fetur da aka yi ya jawo farashin fetur ya karu da kusan N700 a cikin watanni haka kudin gas da ake saye domin girki ya tashi.

Mafi yawan al'ummar Najeriya su na faman kokawa a game da 'dan karen tsadar rayuwa yayin da Bola Tinubu ya nke ba al'umma hakuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel