Aikin Gwamnatin Najeriya
An raba sama da Naira tiriliyan 6 daga asusun tarayya na FAAC a shekarar bara. Mun kawo bayanin kudin da aka ba kowane Gwamna daga FAAC a shekarar ta 2023.
An samu wasu bayanan sirri kan dalilin da ya sa aka samu tsaiko wajen rantsar da sabbin alkalan Kotun Koli su 11 da majalisar dattawa ta tantance su a watan Disamba.
Ma'aikatan tarayya sun fara 'yan guna-guni yayin da gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na yin albashi a ranar Alhamis, kuma ba a biya su naira dubu 35 ba.
Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya umurci dukkanin ciyamomin kananan hukumomin jihar da su rinka sa hannu a na'urar shaidar zuwa aiki sau hudu a rana.
Ministan ayyuka ya haramta tallace-tallace a hanyoyi, ya bada dalilin maka su a kotu. Dave Umahi ya tura dogarai sun kamo mutanen da ke kasuwanci a babbar hanya
Bola Ahmed Tinubu ya dauko ma’aikata na musamman da za su sa ido a kan ayyukan Ministocinsa. Hadiza Bala-Usman za ta jagoranci auna kokarin ministocin kasar.
Bola Tinubu ya fitar da kudi domin aikin hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano. Gwamnatin tarayya ta dauko ayyuka titunan ne lokacin Muhammadu Buhari yana ofis.
An fadawa Bola Tinubu za ta yiwu Legas ta zama kishiyar birnin tarayya ba. SanataAli Ndume bai goyi bayan a kinkimi wasu ofisoshin gwamnatin tarayya zuwa Legas ba.
Bola Tinubu ya dauki alkawari talaka zai more idan ya kara hakuri. Shugaban kasa ya gana da wasu Sarakuna a fadar Aso Rock Villa, yace masu dadin yana gaba.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari