Gwamnatin Tinubu Za Ta Ba Da Bashin Naira Biliyan 75 Ga Talakawan Najeriya

Gwamnatin Tinubu Za Ta Ba Da Bashin Naira Biliyan 75 Ga Talakawan Najeriya

  • Gwamnatin Tinubu ta kaddamar da wani shiri na bayar da bashin naira dubu hamsin ga kanan da matsakaitan 'yan kasuwa har mutum miliyan 1.5
  • Shirin MSME zai zama kamar ci gaban shirin "Market-Moni" ne, shirin da gwamnati ta kafa don tallafawa 'yan kasuwa
  • Haka zalika, gwamnatin tarayyar za ta kaddamar da wani sabon shiri da zai bunkasa rayuwar talaka a wata mai kamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Domin tallafawa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa, gwamnatin Tinubu ta kaddamar da shirin "Renewed Hope Micro, Small and Medium Enterprise (MSME)".

An kaddamar da shirin MSME don fadada shirin "Market-Moni", da nufin tallafawa talakawa miliyan 1.5 da jarin naira dubu 50 kowanne mutum daya.

Kara karanta wannan

Wike: N15bn ake bukata a karasa gidan mataimakin shugaban kasa da aka fara a 2013

Uwar gidan Tinubu da Minista Edu wajen shirin MSME
Shirin MSME na daga cikin kokarin Shugaba Tinubu na kawar da talauci, da kuma tallafawa 'yan Najeriya miliya 1.5 da kudin da za su yi sana'a. Hoto: Felix Onigbinde
Asali: Twitter

A baya, an fi sanin shirin da suna "shirin tallafawa talakawa 'yan kasuwa na gwamnati (GEEP)", kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin MSME zai tallafawa 'yan Najeriya miliyan 1.5 da kudin jari - Edu

Rahotanni sun bayyana cewa uwar gidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ce ta kaddamar da shirin a Abuja, inda ta raba takardun ceki ga wadanda za su ci gajiyar shirin.

Ministar jin kai da kawar da fatara, Dakta Betta Edu, ta tabbatar da cewa duk wanda ya yi rijistar kasuwancinsa, kuma aka tantance shi, zai samu tallafin naira dubu hamsin.

Ta ce shirin na daga cikin kokarin Shugaba Tinubu na kawar da talauci, da kuma tallafawa 'yan Najeriya miliya 1.5 da kudin da za su yi sana'a.

Gwamnatin Tinubu za ta bullo da sabon shiri wata mai kamawa - Edu

Kara karanta wannan

"Abin duniya ke rudar 'yan Najeriya", Buhari ya yi magana mai jan hankali kan zabukan shugaban kasa

"Dole in nanata cewa shugaban kasa zai kawo babban canji a Najeriya nan da shekara mai zuwa.
"Muna da shirye-shiryen, irin su N-Power, ciyar da dalibai abinci, da kuma shirin abin hawa na kawar da yunwa wanda Tinubu zai kaddamar wata mai kamawa."

- Betta Edu.

Uwar gidan shugaban kasar ta yi nuni da cewa, shirin MSME zai taimakawa marasa karfi da tallafin da za su dogara da kansu, har su fita daga kangin talauci.

Yadda ’yan Najeriya za su samu damar yin karatu kyauta a Faransa

A wani labarin, ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya, ya sanar da bayar da cikakken tallafin karatu ga daliban kasar don ci gaba da karatun digiri, Legit Hausa ta ruwaito.

Wannan damar ta hada da tallafin sufuri, alawus-alawus na wata-wata, shawarwari kan gidajen zama, kula da lafiya, kudaden biza, da kuma kudaden karatun kasar

Asali: Legit.ng

Online view pixel