Tinubu Ya Ba Ministan ‘Yaradua da Wasu Mutum 9 Mukami a Gwamnatin Tarayya

Tinubu Ya Ba Ministan ‘Yaradua da Wasu Mutum 9 Mukami a Gwamnatin Tarayya

  • Sanarwa ta fito cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi nadin sababbin mukamai a ma’aikatar kudi da tattalin arziki
  • Ajuri Ngelale ya ce Mai girma shugaban kasa ya nada wadanda za su jagoranci ragamar kamfanin MOFI na kasa
  • Dr. Armstrong Ume Takang shi ne shugaban MOFI, yayin da Dr. Shamsudeen Usman zai sa ido wajen gudanarwa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin mutane goma da za su zama Shugabannin da za su rika sa ido a aikin kamfanin MOFI.

Sanarwar nadin mukaman ta fito ne daga ofishin mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale.

Cif Ajuri Ngelale ya ce Dr. Shamsudeen Usman ne zai jagoranci majalisar MOFI a Najeriya, mukamin da yake kai tun farkon shekarar nan.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisa ya fito a bidiyo ya cika baki APC za ta karbe Gwamna hannun PDP a Kotu

Tinubu
Bola Tinubu ya nada shugabannin MOFI Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene wadanda Bola Tinubu ya nada a MOFI:

(1) Dr. Shamsudeen Usman — Shugaban majalisar sa ido

(2) Dr. Armstrong Ume Takang — CEO/Babban Darekta

(3) Mr. Tajudeen Datti Ahmed — Babban Darekta, Portfolio Management

(4) Mr. Femi Ogunseinde — Babban Darekta, Kula da hannun jari

(5) Mrs. Oluwakemi Owonubi — Babban Darekta, kula da hadari

(6) Mrs. Fatima Nana Mede — Darekta

(7) Mr. Ike Chioke — Darekta

(8) Ms. Chantelle Abdul — Darekta

(9) Mr. Alheri Nyako — Darekta

(10) Mr. Bolaji Rafiu Elelu — Darekta

MOFI: Tinubu ya dauko mutane daga ko ina

Legit ta duba jerin, ta lura an zabo sauran shugabannin ne daga kowane yanki na kasar nan.

Jerin ya na kunshe da maza bakwai da mata uku wadanda za su zama Darektoci a kamfanin da ke karkashin ma’aikatar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fayyace ainihin sababin tsige Abba, gwamnan Filato a Kotu

Kamar yadda Leadership ta kawo rahoton, sanarwar ta ce Mai girma Bola Tinubu yana son ganin cigaba a kamfaonin gwamnatin tarayya.

Ngelale yake cewa Tinubu ya na sa ran shugabannin za su gudanar da aikinsu da kyau a MOFI.

Bushahar Tinubu da gwamnonin Jihohi

Bincike ya nuna irin kudin da gwamnoni har da gwamnatin tarayya su ke kashewa wajen gudanar da aiki duk da ana kukan karancin kudi.

A watanni 9, Gwamnonin jihohi sun batar da tiriliyoyi a alawus, tufafi, sayen kaya da tafiye-tafiye, albashin da aka biya ma’aikata ya kai N800bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel