Ofishin Jakadacin Kanada Ya Dakatar Da Ayyukansa a Najeriya, Ya Fitar Da Gargadi

Ofishin Jakadacin Kanada Ya Dakatar Da Ayyukansa a Najeriya, Ya Fitar Da Gargadi

  • A ranar Litinin, kasar Kanada ta sanar da dakatar da dukkanin ayyukanta a Najeriya har zuwa wani lokaci da ba ta bayyana ba
  • Wannan sanarwar na zuwa ne awanni bayan da wani sashe na ofishin jakadancin Kanada ya kamata da wuta a Abuja, lamarin da ya jawo asarar rayuka da jikkata wasu
  • Kanada ta kuma gargadi 'yan kasarta da su kaurace wa shiga Najeriya a wannan lokaci sakamakon matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Litinin, Kanada ta dakatar da duk wasu ayyuka da ta ke yi a Najeriya har zuwa wani lokaci da ba ta bayyana ba. Haka zalika kasar ta bi sahun Amurka da Birtaniya na yi wa 'yan kasarta kashedin zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar sayar da kayan Samsung a Abuja

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bola Tinubu a cikin wata sanarwa ya ce an samu asarar rayuka da raunuka a gobarar da ta tashi a ofishin jakadancin kasar Kanada a ranar Litinin, sai dai bai fadi adadin mutanen da abin ya shafa ba.

"Shugaba Tinubu na mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan samun lafiya ga wadanda suka jikkata".

A cewar sanarwar.

Kanada da Najeriya
Kasar Kanada ta kuma gargadi al'umarta da su kaurace wa shiga Najeriya saboda matsalar tsaro Hoto: Betta Edu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai jakadan kasar Kanada a Najeriya bai yi tsokaci kan gobarar ba, amma dai ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Mun dakatar da dukkan ayyuka har sai nan gaba idan mun sanar."

Ofishin jakadancin ya kuma gargadi ga wadanda ba a Najeriya su ke ba, da su kaurace wa shigo wa kasar, "sakamakon matsalar rashin tsaro da ta kara tabarbarewa a kasar, da kuma fargabar ayyukan ta'addanci, garkuwa da mutane, fadan kabilanci ko addini, fashi da makami da sauransu."

Kara karanta wannan

Sarkin Legas ya bai wa Tinubu, Atiku da Peter Obi muhimmin shawara bayan hukuncin kotun koli

Kasashen Yamma na hana al'ummarsu zuwa Najeriya

Tinubu, ya mayar da hankali a yanzu wajen gyara tattalin arziki, ba tare da fayyace hanyoyin da zai bi wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar ba, wadanda sukahada da ta'addancin Boko Haram a Arewa maso Gabas, da kuma garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma.

A ranar Juma'a kasar Amurka da Burtaniya suka fitar da sanarwar hana 'yan kasarsu shiga Najeriya musamman akan cewar za a iya samu hare-hare a manyan otel-otel na kasar, kamar yadda wakilin Reuters ya ruwaito.

A baya bayan nan dai, kasashen Yamma da ke da jakadanci a Najeriya na ci gaba da gargadar al'ummarsu da su kauracewa zuwa Najeriya a irin wannan lokaci, kashedin da gwamnatin Najeriyar kullum ke karyatawa, bisa cewar babu hujja kan hakan.

Ofishin jakadancin Kanada ya kamata da wuta

A jiya Litinin, 6 ga watan Nuwamba, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa wani bangaren ginin ofishin jakadancin kasar Kanada a Najeriya ya kama da wuta rigi-rigi a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wasu sassan ofishin jakadancin Kanada wanda ke a lamba 13010G Palm Close, Diplomatic Drive, Central Business District a Abuja ne suka kama ci da wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel