Kashim Shettima
Gwamnoni sun nuna rashin jin dadin yadda Bola Tinubu ya dauko abokin takararsa. Hakan ta sa dole Gwamnonin APC sun yi zama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon Sanata ya wanke Kashim Shettima daga zargin alaka da ‘Yan Boko Haram. Ana tuhumar 'dan takaran APC da hannu wajen rikicin Boko Haram da sace 'Yan Chibok.
Babachir Lawal ya yi kaca-kaca da Bola Tinubu a kan dauko abokin takara Kirista. Tsohon Sakataren Gwamnatin bai goyon bayan takarar Sanata Kashim Shettima.
Shahararren dan siyasa Adamu Garba ya sake komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki bayan ya sauya sheka zuwa Young Progressives Party (YPP).
Ali Modu Sheriff ya ce ya sanyawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima albarka.
Manyan jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun taya Sanata Kashim Shettima murnar zabarsa da aka yi a matsayin mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.
Festus Keyamo ya yabi zabin Sanatan Borno, Kashim Shettima da Bola Ahmed Tinubu ya yi, Keyamo yake cewa Sanata Shettima yana da biyayya, sannan ya san aiki.
Sanata mai wakiltan yankin Adamawa ta arewa, Ishaku Abbo, ya yi murabus daga kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Mai Buni na jihar Yobe ya yabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, bisa zabin abokin takararsa, Kashim Shettima a jiya.
Kashim Shettima
Samu kari