Babachir: APC Ba Za Ta Kai Labari Ba a Zaben Shugaban Kasa Saboda Tsayar Da Musulmi da Musulmi

Babachir: APC Ba Za Ta Kai Labari Ba a Zaben Shugaban Kasa Saboda Tsayar Da Musulmi da Musulmi

  • Babachir Lawan ya ce Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ba zai yi nasara ba a zaben 2023 saboda tikitin Musulmi da Musulmi
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya yi zargin cewa ana nuna ma kiristocin arewacin Najeriya wariya a yankin
  • Babachir ya jaddada cewa shi ba zai yi Tinubu ba a babban zabe mai zuwa don har sun fara tattaunawa da jam'iyyun adawa

Tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawan, ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) ba zata kai labari ba a zaben shugaban kasa na 2023.

Babban jigon na APC ya ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba zai yi nasara a zabe mai zuwa ba saboda zaban Kashim Shettima musulmi dan uwansa da yayi a matsayin abokin takara, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu: Buhari ya jefa Najeriya a yunwa, amma ya yi wani abu 1 da ya kamat kowa ya sani

Shettima da Tinubu
Babachir: APC Ba Za Ta Kai Labari Ba a Zaben Shugaban Kasa Saboda Tsayar Da Musulmi da Musulmi Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

A hirarsa da BBC, Bababchir ya yi ikirarin cewa sun yi iya yinsu domin ganin Tinubu, wanda yake Musulmi ya samu tikitin jam’iyyar amma daga bisani sai suka gano cewa yayi masu shigo-shigo ba zurfi ne a kan wanda zai dauka ya zama mataimakinsa.

Daukar tsohon gwamnan jihar Borno da dan takarar shugaban kasar na APC yayi ya sa Babachir da wasu kiristocin jam’iyyar musamman daga arewa suka juya masa baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba zan yi Tinubu ba a zaben 2023

Babachir ya ce lallai APC ba za ta je ko’ina ba a zaben shugaban kasa kuma faden jihohin da Tinubu zai iya ci da wadanda ba zai iya ci ba.

Ya ce:

“Bana yin Bola Tinubu a yanzu. Ba na goyon bayan takarar Musulmi da Musulmi.
“Shi Tinubu ne bai dauke mu ba ya dauki inda yake so ya je, mun kuma sanar masa tun da farko cewa ba za mu zabe shi ba idan ya kuskura ya yi tikiin Musulmi-Musulmi.”

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Mun tattauna da jam'iyyar PDP da Labour Party

Babachir ya kuma bayyana cewa PDP sun zo sun tuntube su, kuma sun amince za su yi masu abun da suke bukata idan suka ba da hadin kai don haka sun amince za su yi masu.

Hakazalika ya ce kusan kwana jam’iyyar Labour Party suka yi a wajensu suna neman su hada tafiya da su.

Ya kuma bayyana cewa ba shi kadai Tinubu ya yiwa rufa-rufa ba ganin cewa sun tsaya ka’in da na’in wajen ganin ya samu takara, kiristoci gaba daya ya yi wa.

Ana nunawa kiristoci wariya a arewa

Jigon siyasan ya kuma ce babban matsala ce irin ta wariyar da ya yi zargin ana nuwa kirista a arewacin kasar yana mai cewa:

“Ka ga matsalar yan arewan nan a ce kai Kirista ne samun aiki ma wuya yake mana.
“Ka ga daga cikin jami’o’I 27 na arewar nan biyu ne kadai kirista ke shugabanci. Kwalejin jimiya 27 guda biyu ne kadai kirista ke shugaba, na tarayya kenan banda na jihohi.”

Kara karanta wannan

2023: A Karshe Oshiomhole Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Kayar Da Atiku Domin Ya Ci Zaben Shugaban Kasa

Ya koka cewa wariyar da ake nuna wa kiristoci a arewa abun ya yi masu yawa sai kuma a zo ace za yi tikitin Musulmi da Musulmi, “to ka ga kenan an buga mana kusa a ka baya ga wanda aka buga mana a kafa.”

Malamin addini ya bukaci kirisoci da kada su zabi Tinubu a 2023

A wani labarin kuma, mun kawo cewa limamin katolika na Kaduna, Rabaran Mathew Ndagoso ya yi kira ga kiristoci a kan su guji zaban dan takarar shugaban kasa na jam'iyya mai mulki a zaben shekara mai zuwa.

Ndagoso ya ce tikitin Musulmi da Musulmi ya nuna rashin adalcin jam'iyyar don haka dole ta hadu da fushin abun da ta aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel