Kasar waje
Kamfanin Twitter ya yi barazanar maka mai kamfanin Meta, Mark Zuckerberg a kotu bisa zargin satar bayanai na kamfanin ba tare da izini ba, Meta ya musa zargin.
Hukumar alhazai ta jihar Kano ta sanar da rasuwar daya daga cikin maniyyatan jihar, Hadiza Isma'il a Makkah bayan fama da jinya a ranar Litinin 3 ga watan Yuli.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyarta na kakaba yaren China a tsangayoyin jami'o'in kasar da inganta mu'amala tsakanin kasashen guda biyu ta fannoni da dama.
Gwamnatin kasar Sweden ta musanta zargin cewa da hannunta aka kona Alkur'ani mai girma a kasar, ta nuna bacin ranta tare da Allah wadai da wannan aika-aika.
Kungiyar Kasashen Musulmi ta OIC ta ce dole a dauki matakin bai daya don kare Alkur'ani da dakile faruwar hakan, sun yi kira da kafa dokokin kasa akan hakan.
Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta caccaki Turawan EU game da yadda suka kawo rahoton karshe game da zaben 2023 da ya gabata. Ya bayyana bacin ransa game da haka.
Elon Musk ya bayyana adadin rubutun da 'yan Twitter za su ke gani a kowacce rana, sabanin yadda aka saba ganin rubutun yadda yake ba tare da wata matsala ba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa sun shirya a watan Satumba za su fara ba da tallafin karatun dalibai zuwa kasashen waje don inganta ilimi.
Wani mutum, Herbert Baitwababo ya maka mai gudanar da rukunin manhajar 'WhatsApp' a Uganda kan zargin cire shi a rukuni wanda suka kirkira don taimakon al'umma.
Kasar waje
Samu kari