Sweden: OIC Ta Bayyana Matakan Da Za Ta Dauka Don Kare Martabar Alkur'ani, Al-Azhar Ta Ba Da Shawara

Sweden: OIC Ta Bayyana Matakan Da Za Ta Dauka Don Kare Martabar Alkur'ani, Al-Azhar Ta Ba Da Shawara

  • Kungiyar Kasashen Musulmi (OIC) sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani mai girma da aka yi a kasar Sweden
  • Kungiyar ta ce suna ganawa da sauran mambobinsu don samar da mataki bai daya da zai hana faruwar hakan
  • Kungiyar ta bukaci a samar da dokokin kasa da kasa cikin gaggawa don kiyaye nuna wariyar addini

Tun bayan kona Alkur’ani mai girma da aka yi a kasar Sweden, kasashen duniya da dama musamman na Musulmi suke Allah wadai da wanna danyen aiki.

Kungiyar Kasashen Musulmi (OIC) ta yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da ba da shawarar daukar matakai don kauce wa faruwar hakan a gaba.

OIC ta bukaci daukar mataki kan kona Alkur'ani a kasar Sweden
Kungiyar Kasashen Musulmi (OIC). Hoto: OIC.
Asali: Twitter

An gano wani matashi Salwan Momika dan kasar Iraki yana tattaka Alkur’ani kafin ya kona shi a bakin wani masallaci a birnin Stockholm.

Kara karanta wannan

“Kamar a Fim”: Matashiya Ta Auri Hadadden Dan Koriya a Asiya, Hadadden Bidiyon Bikin Ya Zautar Da Yan Mata

Kona Alkur'ani a Sweden ya jawo korafe-korafe daga kasashen duniya

Kungiyar mai mambobi 57 sun gudanar da wata ganawa a Jiddah na kasar Saudiyya don samo martani da kuma matakin da za su dauka kan wannan danyen aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar a jiya Lahadi 2 ga watan Yuli ta shawarci mambobin kungiyar su lalabo matakin bai daya don ganin an kaucewa faruwar hakan a gaba.

A cewar sanarwar:

“Dole muna tunatarwa kasashe game da tabbatar da dokokin kasa da kasa cikin gaggawa wanda zai haramta kiyayya ga addinai daban-daban.”

Jami'ar Al-Azhar ta ba da shawara kan kona Alkur'ani da aka yi a Sweden

Jami'ar Al-Azhar da ke Cairo a kasar Masar ta shawarci Musulmai da kada su dauki wani mataki akan hakan inda suka ce Allah shi zai kare Alkur'ani, Aminiya ta tattaro.

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

Shugaban binciken addinin Musulunci ta jami'ar, Sheikh Ahmed Mohammed ne ya ba da wannan shawara inda ya ce kada Musulmai su sabawa koyarwar addininsu saboda wautar wasu mutane.

Wannan shawarar ta jami'ar Al-Azhar na zuwa ne kwanaki kadan bayan an kona Alkur'ani a Sweden wanda ake zargin hakan ya samu daurin gindi daga kotu da kuma 'yan sanda.

Ya kara da cewa Musulmi su kwantar da hankalinsu kada su yi wani kone-kone ko kashe-kashe tunda ubangiji ya yi alkawarin kare Alkur'ani mai girma, cewar Aljazeera.

Fastoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani A Sweden

A wani labarin, Fastoci a Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da aika-aikan da aka yi a kasar Sweden.

Fastocin suka ce sun shirya tsaf don kare martabar Alkur'ani a ko ina suke kuma a ko yaushe.

Sun roki Musulmi da su yi koyi da koyarwar addinin Musulunci na zaman lafiya don gudun daukar fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel