Tinubu Ya Dawo Najeriya, An Hango Shi Tare da Gbajabiamila, Ganduje a Filin Jirgi

Tinubu Ya Dawo Najeriya, An Hango Shi Tare da Gbajabiamila, Ganduje a Filin Jirgi

  • Bola Ahmed Tinubu ya iso Najeriya bayan an gama taron kungiyar ECOWAS a Guinea Bissau
  • Shugaban Najeriyan ya yi kwanaki biyu a kasar Afrikan, a yammacin jiya ne ya dawo Aso Rock
  • A birnin Bissau ne shugabannin kasaashen Afrika ta yamma su ka zabi Tinubu ya rike ECOWAS

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A yammacin Litinin ne aka ji Bola Ahmed Tinubu da ‘yan tawagarsa sun dawo Najeriya bayan halartar taron ECOWAS a Guinea-Bissau.

Rahoton da mu ka samu daga Tribune ta sanar da cewa bayan an kammala zaman kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu ya iso garin Abuja dazu.

Shugaban Najeriyan ya dawo gida ne da kimanin karfe 6:30 na yamma, ya sauka a babban tashar jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Yi Jawabi da Jin Tinubu Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya dawo daga Bissau Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Rt. Hon. Gbajabiamila sun yi masa maraba

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci wadanda su ka yi wa Mai girma shugaban Najeriyan maraba da dawowa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce Abubakar Atiku Bagudu, Abubakar Badaru da Abdullahi Umar Ganduje da wasu jami’an gwamnati su na cikin wadanda su ka tarbe shi.

Kamar yadda aka bada sanarwa a baya, da zarar an gama wannan muhimmin taro a birnin Bissau, shugaban kasa Tinubu zai koma bakin aiki a Abuja.

This Day ta ce jirgin fadar shugaban kasa na NAF 001 kirar Boeing 737 ya kai kuma ya dawo da Tinubu daga kasar Afrika ta yammar ya kai wa ziyara.

Tinubu zai rike kungiyar ECOWAS

Daga zuwansa taron ECOWAS na farko, sai aka ji har an zabi Tinubu a matsayin shugaban kungiyar kasashen na yammacin Afrika mai tsohon tarihi.

Kara karanta wannan

Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS

Dele Alake ya ce hakan ya nuna yadda kasashen na Afrika su ka yi amanna da shugaban Najeriya.

Abin kunya a filin jirgin Legas

Watanni tara da aka kashe kudi wajen samar da na’urorin haskaka filin tashin jirgin Murtala Muhammad, sai ga rahoto cewa wasu sun sace kayan aikin.

Tribune ta ce ana zargin barayi sun yi amfani da damar da aka samu na rufe tashar, su ka hada-kai da ma’aikata, aka sace fitilun da ke tashar jirgin na Legas.

Ganduje zai zama Minista?

Hakan ya na zuwa ne a lokacin da ake rade-radin cewa akwai wasu tsofaffin Gwamnoni biyar da za su samu kujerar Minista a sabuwar gwamnati.

A gefe guda, an samu kungiyoyi da jama’a da ke musayar baki, su na bada shawarar cewa shugaba Tinubu ya nesanta kan shi daga irinsu Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel