Kano: Abba Gida Gida Ya Fadi Lokacin Da Tallafin Karatu Na Dalibai Zuwa Kasashen Waje Zai Fara Aiki

Kano: Abba Gida Gida Ya Fadi Lokacin Da Tallafin Karatu Na Dalibai Zuwa Kasashen Waje Zai Fara Aiki

  • Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana lokacin da rukunin farko na dalibai masu tafiya kasashen waje za su fara karatu
  • Gwamnan ya ce sun shirya tsaf don ganin rukunin farko na daliban sun fara karatu a jami'o'i daban-daban zuwa watan Satumba
  • Gwamna Abba Kabir shi ya bayyana haka yayin ziyarar da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kai masa na murnar bikin sallah

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa rukunin farko na tallafin karatun kasashen waje zai fara ne a watan Satumba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren rikon kwarya na yada labaran gwamnan, Hisham Habib a ranar Asabar 1 ga watan Yuli a Kano.

Abba Gida Giida ya fadi watan da za a fara ba da tallafin karatu zuwa waje a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Abba Gida Gida ya bayyana haka yayin ziyarar da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kawo masa a ranar sallah.

Kara karanta wannan

Don ku nake yi: Abba Gida-Gida ya fadi gaskiyar dalilin rushe-rushen da yake a Kano

Abba ya ce za su inganta harkar ilimi a Kano don dalibai su samo abin dogaro

Gwamnan ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da inganta harkokin ilimi a jihar, Daily Trust ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa shirye-shirye sun kankama don sake bude manyan makarantu guda 20 da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta rufe.

Gwamnan ya godewa Sarkin, inda yabawa sarakunan gargajiya kan gudumawar da suke bayarwa a fannin kawo zaman lafiya.

Sarki Bayero ya roki gwamnan akan samar da takin zamani a Kano

Tun farko a jawabinsa, Sarki Bayero ya roki gwamnan ya samar da takin zamani ga manoma a farashi mai rahusa, cewar Daily Nigerian.

Ya kuma bukaci da a ci gaba da shuka bishiyoyi don rage zaizayar kasa tare da samar da ruwan sha a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Muhimman Alkawura 3

Ya kirayi gwamnatin da ta yi duk mai yiyuwa don inganta tattalin arziki don masu zuba hannun jari wanda zai kawo ci gaba a jihar Kano.

Mun Kashe Biliyan 20 Kan Tallafin Karatu, Ganduje Ya Mayar Wa Abba Kabir Martani

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsu ta kashe makudan kudade kan tallafin karatu.

Ganduje ya ce akalla sun kashe fiye da N20bn a lokacin mulkinsu don inganta ilimi a jihar.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin mayar da martani ga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Online view pixel