Dukiya Ta Ƙara Yin Gaba, Aliko Dangote Ya Samu Naira Biliyan 600 Cikin Awa 24

Dukiya Ta Ƙara Yin Gaba, Aliko Dangote Ya Samu Naira Biliyan 600 Cikin Awa 24

  • Aliko Dangote ya tabbata a matsayinsa na Attajirin da ya fi kowa kudi a fadin nahiyar Afrika
  • Rahoton Forbes ya nuna an yi shekaru 12 kenan a jere, babu wanda ya sha gaban ‘Dan Najeriyan
  • Dangote ya samu N613.3bn a cikin sa’o’i 24, a halin yanzu dukiyar da ya mallaka ta zarce $16bn

Abuja - Aliko Dangote ya koma matsayinsa na mai kudin nahiyar Afrika. Forbes ta ce ‘dan kasuwan ya sha gaban Johann Rupert.

Legit.ng ta ce ‘Dan kasuwan kasar Afrika ta Kudun, Johann Rupert ya shafe makonni biyu a matsayin wanda ya fi kowa arziki a nahiyar.

A cikin masu arzikin Duniya, Dangote ne kurum mutumin Najeriya a sahun manyan Attajirai, a halin yanzu shi ne na 124 a jerin Forbes.

Aliko Dangote
Aliko Dangote yana jawabi a Ghana Hoto: Getty / Ernest Ankomah
Asali: Getty Images

An sha gaban Johann Rupert

Kara karanta wannan

NLC Za Ta Sa Ƙafar Wando Ɗaya da Bola Tinubu, An Buƙaci Karin 300% a Albashi

Wanda yake biye da Dangote mai shekara 626 da haihuwa shi ne Mista Rupert mai $11.1bn, a yanzu shi ne mutum na 157 a masu kudin Duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bloomberg ta na hasashen dukiyar Dangote a kimanin $16.9bn, a cikin makonni 14 da suka gabata, ya samu karin $2bn a kudin da ya mallaka.

A cikin sa’o’i 24 na makon nan, arzikin ‘dan kasuwan ya karu da 5.8% bayan karya Naira da gwamnatin Najeriya tayi jawo ya rasa biliyoyi.

Mike Adenuga ya rasa $2.7bn

Yayin da Attajirin Najeriyan ya samu makudan kudi a farkon watan Yuni, shi kuma Mike Adenuga ya yi asarar abin da ya kai Dala biliyan 2.7

Mista Adenuga shi ne shugaban kamfanin Globacom, ya mallaki sama da Dala biliyan 3.

A ina Dangote ya samu dukiyarsa?

Aliko Dangote ya yi kudi ne da siminti, shi ya fi kowa shahara a kasashen nahiyar Afrika, shi ya mallaki 85% na kamfanin 'Dangote Cement.'

Kara karanta wannan

Bude Iyakokin Najeriya: Shugaban Kwastam Ya Yi Magana Bayan Zaman Farko Da Tinubu

Forbes ta ce a shekara, kamfaninsa na iya samar da metric ton miliyan 48.6 a kasashen Kongo, Ghana, Tanzaniya, Sanagal da su Zambia.

A halin yanzu Dangote ya na kammala ginin matatar mai a Legas, wanda yake sa ran a duk rana za ta iya tace gangunan danyen mai 600, 000.

CBN ya jawo Dangote ya rasa N1.4tr

Kwanakin baya rahoto ya zo cewa hamshakan masu kudin Najeriya sun rasa Biliyoyin Daloli tun da bankin CBN ya saki Naira a kasuwa.

A lokacin da masana tattalin arziki su ke yabawa Bola Tinubu, lokacin wasu su ka tafka asara. Aliko Dangote ya rasa N1.4tr cikin 'yan kwanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel