
Department Of State Security (Dss)







Shugabannin kungiyoyin ƙwadago sun ce ba gudu ba ja da baya daga kudirin da suka yi na gudanar da zanga-zanga a ranar 27 da 28 ga watan Fabrairu a fadin Najeriya.

Sababbin bayanai sun fito bayan bacewar shugaban 'yan Miyetti Allah Kautal Hore a Nasarawa. Hukumar DSS tace ba ta tsare da shugaban kungiyar makiyayan.

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta kasa sun cafke shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Haure, Bello Bodejo, kan kafa kungiyar ‘yan banga a Nasarawa.

Wani ‘dan Majalisar NNPP ya ce DSS ta saki Bawan Allah bayan shekara 9 yana hannun hukuma. Kotu ta ce a saki Malam Isa Umar amma har yau bai fito ba.

Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufuri, ya ce DSS sun dakile shirin dakarun soji na yin juyin mulki zamanin Shugaba Muhammadu Buhari. Ya kuma jinjinawa Yusuf Bichi

Tsohon shugaban hukumar NIRSAL ya na hannun jami’an tsaro. Ana zargin ya tsere da motocin ofis 32 bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kore shi daga aiki.

Bayan shekaru takwas, wata babbar kotu da ke Ikeja, jihar Legas, ta yanke wa wani hukuncin kisa bisa kama shi da laifin kashe jami'an DSS guda 7..

DSS suna ta sintiri a rumfar zaben da ake tsammanin Dino Melaye zai jefa kuri’arsa a yau bayan an samu ma’aikatan tattare da takardun da aka rubuta sakamako.

Ana da labari an tsare tsohon Gwamnan bankin CBN na wata da watanni duk da kotu ta ce a sake shi. Alkali ya bukaci EFCC ta gaggauta sakin Mr. Godwin Emefiele.
Department Of State Security (Dss)
Samu kari