'Dan Majalisa Ya Bukaci DSS Ta Fito da Dalibin ABU da Aka Tsare Na Shekaru Kusan 10

'Dan Majalisa Ya Bukaci DSS Ta Fito da Dalibin ABU da Aka Tsare Na Shekaru Kusan 10

  • Abdulhakim Kamilu Ado Isa ya gabatar da korafi a majalisar wakilan tarayya a kan jami’an hukumar DSS
  • ‘Dan majalisar na Kano ya ce DSS sun kama wani dalibi mai suna Isah Umar tun 2014, sun tsare shi
  • Hon. Abdulhakim Kamilu Ado ya bukaci ‘yan majalisa su yi amfani da matsayinsu wajen fito da matashin

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Abdulhakim Kamilu Ado Isa ya mike a zauren majalisar tarayya, ya bukaci a saki wani da yake tsare a hannun DSS.

‘Dan majalisar mai wakiltar Wudil da Garko ya ce tun shekarar 2014 aka cafke wani Isa Umar, har yau dai babu labarinsa.

'Dan Majalisa
Zaman 'Yan Majalisar wakilan tarayya Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

A wani bidiyo da aka gani a Facebook, Hon. Abdulhakim Kamilu Ado Isa ya ce wanda aka dauke dalibi ne a jami’ar ABU Zariya.

Kara karanta wannan

Atiku, Amaechi, Shekarau, Binani da jiga-jigan ‘yan siyasa da suka fi kowa asara a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Abdulhakim Kamilu Ado Isa yake cewa wani Aliyu Umar ne ya kawo korafin hukumar DSS masu fararen kaya a Najeriya.

DSS ta kama Bawan Allah

A jawabin da ya yi a gaban majalisa, ‘dan siyasar ya ce ana zargin jami’an tsaro da tsare Isa Umar ba tare da bin dokar kasa ba.

Tun ranar 26 ga watan Nuwamba 2014 aka yi ram da Isa Umar wanda ‘dan majalisar ya ce mutumin kwarai ne da bai yi laifi ba.

‘Dan siyasar yake cewa ana zargin jami’an da su ka dauke wannan matashi, sun mika shi ne a hannun hukumar tsaro ta DSS.

Hukumar DSS ta sabawa umarnin kotu

Da aka je kotu, Abdulhakim Kamilu Ado ya ce alkali ya umarci hukuma ta fito da dalibin tare da cin tararta saboda saba doka.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan PDP da APC da su ka halarci zaman sulhun da Tinubu yayi wa Wike da Fubara

‘Dan majalisar na Kano ya fadawa shugaban majalisar wakilai cewa har zuwa makon nan, DSS ba ta bi umarnin kotun ba.

Wanene Isah Umar?

Mazauna unguwar Samaru a garin Zariya sun shaidawa Legit jama’a sun fi sanin Isa Umar da Isa Pele saboda wasan kwallon kafa.

Wadanda su ka san shi sun ce matashin yana da kokarin addini, yanzu shekaru kusan 10 kenan babu wanda ya sake ganin shi.

Wanda yake tsaren yana aji uku ne a jami’a, saura shekara guda ya kammala digiri.

Abokan Isa Umar sun yi magana

Wani abokinsa ya ce an bada belinsa tun 2017 da aka samu labari DSS ta kama shi, amma har yanzu yana makargama na shekara da shekaru.

‘Yanuwa da abokan arziki sun yi ta kokarin ganin an fito da shi, amma ba a dace ba.

“Isa Umar shi ne Amir dinmu a makarantar ITN. A 2012 aka kama shi da wasu abokan karatanmu a masallacin Khalid Bin Walid da sunan cewa su ‘yan Boko Haram ne.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar NNPP ya kuma taimakawa mata 500 da kudi a mazabarsa a Jihar Kano

Bayan ‘yan makonni aka fito da su, aka fito da shi ya dawo ya cigaba da karatunsa. A Nuwamban 2014, aka sake kama shi a dakin mahaifiyarsa, ba a sake ganinsa ba.”

A cewarsa:

“Mu dai a saninmu da Malam Isa Umar, shi mutum ne mai son addini da kuma kamewa. Yana da mu'amala mai kyau. Yana kokari wajen karantar da addini musamman karatun Alqur'ani.

Ba mu san wani mugun hali ko aqida tare da shi ba gaskiya.

Ina Dadiyata?

Tun a 2019 aka samu labari cewa wasu mutane da ba a san su ba, sun yi awon gaba da Abubakar Idris da aka fi sani da Dadiyata.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano ta ce ana cigaba da bincike kan Malam Abubakar Idris (Dadiyata) da fatan gano inda yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel