Ana Dab da Fara Azumi, Hukumar DSS Ta Aika da Sabon Gargadi Ga 'Yan Najeriya

Ana Dab da Fara Azumi, Hukumar DSS Ta Aika da Sabon Gargadi Ga 'Yan Najeriya

  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fitar da wani sabon gargaɗi a ranar Juma’a, inda ta shawarci ƴan Najeriya da su guji cunkoson jama’a ko wuraren da ake cunkoso
  • Peter Afunanya, mai magana da yawun DSS, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan game da matsalolin tsaron jama’a
  • Dangane da azumin watan Ramadan na Musulmi da kuma lokacin Lent na Kiristoci, Afunanya ya buƙaci jama'a da su bayar da rahoton abubuwan da ba su yarda da su ba a yayin gudanar da ibadunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadi ƴan Najeriya da su guji cunkoson jama’a domin rage haɗurran da ka iya aukuwa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fallasa gaskiya, ya faɗi kuskuren da ake tafkawa kan matsalar tsaro da talauci

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bukaci ƴan Najeriya da su kasance masu lura da abubuwan da za su cutar da jama’a, musamman abubuwan fashewa.

Kakakin DSS, Peter Afunanya
DSS ta ja kunnen 'yan Najeriya Hoto: Peter Afunanya
Asali: Twitter

Afunanya ya buƙaci jama'a da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ga jami'an tsaro ba tare da ɓata lokaci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shawarci malaman addini da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su guji cin riba a lokacin waɗannan muhimman ibadun.

Ya kuma jaddada muhimmancin haƙuri da juna, samar da ƴan uwantaka, tattaunawa, da zaman lafiya a tsakanin jama'a.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ana shawartar jama'a da su kasance masu sanya ido kan abubuwan da za su iya cutar da su musamman abubuwan fashewa.
"Hakazalika, jama'a su san abubuwan da ka iya kawo musu barazana, su bar wurare masu cunkoso ko waɗanda ba su yarda da su ba. Su kai rahoto kan duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ga jami'an tsaron da suka dace.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris ku ji daɗi" Shugaba Tinubu ya aika saƙo ga ƴan Najeriya, ya kaddamar da sabon shiri

DSS ta yi kira da a mutunta addinan juna

Ya ƙara da cewa hukumar ta DSS ta fahimci muhimmancin waɗannan ibadu, sannan ya buƙaci masu ibada da su ƙara fahimtar juna, tausayi da mutunta juna a lokacin gudanar da ibadunsu.

Kakakin na DSS ya yi wa mabiya waɗannan addinai fatan zaman lafiya, haɗin kai da lumana.

Shugabannin ƙwadago sun caccaki DSS

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago sun yi wa hukumar tsaron farin kaya (DSS) martani kan yunƙurin hana su gudanar da zanga-zanga a faɗin Najeriya.

Shugabannin kwadago sun ce ba gudu ba ja da baya daga kudirin da suka yi na gudanar da zanga-zanga a ranar 27 da 28 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel