Muhimman Hanyoyi 6 Mafiya Sauki da Mutum Zai Sauke Alkur’ani a Kwanakin Watan Ramadan

Muhimman Hanyoyi 6 Mafiya Sauki da Mutum Zai Sauke Alkur’ani a Kwanakin Watan Ramadan

  • Mafi yawan Musulmai suna son ganin sun haddace Alkur’ani mai tsarki a cikin watan Ramadana sai dai ba su samun dama
  • Mafi yawan wadanda ke gagara sauke Alkur’anin basu samu tsari ba ne yadda za su sauke littafin mai tsarki cikin sauki
  • A wannan rahoton, mun kawo muku yadda Musulmi zai sauke Alkur’ani daga sau daya har zuwa saukewa shida a cikin watan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yayin da aka shiga watan Ramadan mai alfarma da ake bukatar komawa ga ubangiji, akwai abubuwa da dama da za su taimakawa mutum cimma nasarori.

A watan azumi mafi yawan mutane suke komawa ga ubangiji domin samun yardar Allah tare da yawaita ibada da ambaton Allah domin samun tsira a gobe kiyama, cewar Mishkah Academy.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta kama Musulman da ke cin abinci a bainar jama'a ana azumi

Hanyar sauke Alkur'ani mai girma cikin sauki a watan Ramadana
Hanyoyin da Musulmi zai sauke Alkur'ani cikin sauki a watan Ramadan. Hoto: @FarisHammadi, MuslimSG.
Asali: Twitter

Muhimmancin karatu da sauke Alkur'ani a Ramadan

Daga cikin aikin alheri da mutane suka fi yi shi ne karatun Alkur’ani mai tsarki wanda wasu ke samun daman sauke littafin mai tsarki har zuwa karshe yayin da wasu ke ganin zai yi wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malaman Musulunci su na kiran Musulmi da su ninka karatun Alkur'ani mai tsarki musamman a lokacin watan Ramadan domin samun lada da kuma farin ciki sanadin karanata shi.

Malaman sun na kuma horar mabiya da su ci gaba da ayyukan alheri da suke yi a watan Ramadan har zuwa watan saboda dorewa kan tafarki mai kyau.

Wannan rahoto zai kawo muku yadda zaku sauke Alkur’ani cikin sauki ba tare da shan wahala ba, kamar yadda Faris Hammadi ya wallafa a shafin X.

Sannan Musulmi zai iya sauke Alkur’anin har sau biyu ko uku ko hudu har zuwa sau shida a cikin watan na Ramadan ba tare da shan wata wahala ba ganin yadda hakan ke da tasiri.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar alƙur'ani sun turo saƙo mara daɗi

MuslimSG ta jero yadda za ka sauke Alkur’ani a cikin watan Ramadan cikin sauki domin samun albarkar watan:

Jadawalin yadda mutum zai sauke Alkur'ani a Ramadan

Yawan saukewa a watashawan shafuka a kullumkarantawa bayan kowace sallalokacin da zai dauka
1shafuka 20shafuka 4 sau 5mintuna 4 sau 5
2shafuka 40shafuka 8 sau 5mintuna 8 sau 5
3shafuka 60shafuka 12 sau 5mintuna 12 sau 5
4shafuka 100shafuka 20 sau 5mintuna 20 sau 5
5shafuka 120shafuka 24 sau 5mintuna 24 sau 5
6shafuka 140shafuka 28 sau 5mintuna 28 sau 5

An sanar da ganin watan Ramadan

Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin watan Ramdan a daren ranar Lahadi 10 ga watan Maris.

Mai Alfarma Sultan ya bayyana ganin watan ne bayan rahotanni da aka samu na ganin watan a bangarori da dama a jihohin Najeriya inda ya yi fatan alheri ga al'ummar Musulmin kasar.

Wannan sanarwar ita ke tabbatar da fara azumin watan Ramadan wanda aka yi a ranar Litinin 11 ga watan Maris wanda zai dauki tsawon kwanaki 29 ko 30.

Asali: Legit.ng

Online view pixel