Babu ruwanmu: Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Bai Hannunmu Inji Jami’an DSS

Babu ruwanmu: Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Bai Hannunmu Inji Jami’an DSS

  • Hukumar DSS tace ba ta tsare da shugaban kungiyar makiyayan nan ta Miyetti Allah Kautal Hore
  • Kafin yanzu an yi ta yada labarai cewa jami’an tsaro masu fararen kaya sun yi ram da Bello Bodejo
  • Yanzu dole a shiga bincike domin gano su wanene suka dauke jagoran kungiyar makiyaya da ke kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar DSS mai fararen kaya ta musanya rahotannin da ke yawo na cewa ta cafke shugaban Miyetti Allah Kautal Hore.

A baya an yi ta yada cewa jami’an tsaro sun kama Bello Bodejo, The Cable tace zuwa yanzu babu kanshin gaskiya a rahoton nan.

Jami'in DSS
Wani jami'in DSS Hoto: Getty Images/AFP/Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

DSS ba ta kama shugaban Miyetti Allah ba

Kara karanta wannan

Ana fargabar rayukan mutane da dama sun salwanta a wani sabon rikici a jihar Arewa

Mai magana da yawun bakin DSS na kasa, Peter Afunanya, ya samu yi wa manema labarai karin haske game da halin da ake ciki a jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Afunanya ya fitar da jawabi a yammacin Talata, ya nesanta kansu da hannu wajen kama shugaban na Miyetti Allah Kautal Hore.

Abin da kakakin jami’an tsaron ya fada kurum shi ne Bello Bodejo bai hannunsu, hakan yana nufin ba a san wanda ya dauke Bodejo ba.

“Bai hannun DSS”

- Peter Afunaya

A ranar Talata, Vanguard ta tabbatar da wannan labari ba tare da wani cikakken bayani ba.

Ina jagoran 'yan Miyetti Allah Kautal Hore?

Da farko ana tunanin an kama Bodejo ne a ofishin ‘yan kungiyar Miyetti Allah da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Ana zargin shugaban makiyayan ya kafa wata rundunar tsaro domin kawo zaman lafiya, wanda hakan ya saba doka da tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu: DSS Ta Kama Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Na Kasa, Dalili, Bayanai Sun Fito

Har zuwa safiyar Laraba da ake tattara rahoton nan, bayanai ba su fito a kan inda jagoran kungiyar makakiyan kasar ya shiga ba.

Bodejo da kungiyar Miyetti Allah

Bodejo wanda ya soki manufar zanga-zangar EndSARS a 2020 ya yi niyyar daukar matasa 4, 000 da za suyi aikin tsaro na sa-kai.

A baya a kan zargin kungiyar Miyetti Allah da tada zaune tsaye, shugaban na ta ya saba wanke ta daga irin wannan tuhume-tuhume.

Sule Lamido v Bisi Akande

A babin siyasa, ana da labari cewa babban jigon adawa a Arewacin Najeriya, Sule Lamido yace jam'iyar APC 'yar haramun din PDP ce.

Sule Lamido yana ganin gwamnatin Buhari ‘yar PDP ce domin hadin-gambiza ya kawo ta mulki domin APC ba ta iya haihuwa ita kadai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel