Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Majalisar Dokokin Tarayya Saboda Abu 1, bidiyo ya bayyana

Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Majalisar Dokokin Tarayya Saboda Abu 1, bidiyo ya bayyana

  • Masu zanga-zanga sun yi tururuwa a majalisar dokokin tarayya domin nuna bacin ransu kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa a Najeriya
  • Shugaban 'yan kwadago ta kasa, Joe Ajaero ne ya yi wa mambobin kungiyarsa jagoranci inda suke kokarin isar da kokensu ga shugabannin majalisar
  • Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta yi wani abu a kan mawuyacin hali da tattalin arzikin kasar ya shiga tun bayan cire tallafin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Babban birnin tarayya, Abuja - Shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Joe Ajaero ya jagoranci dubban masu zanga-zanga zuwa majalisar dokokin tarayya, domin nuna bacin ransu kan tsadar rayuwa a kasar.

An gano jami'an hukumomin tsaro daban-daban girke a hanyoyin shiga da fita daga majalisar, musamman ma a bangaren sakatariyar tarayya domin kula da yadda ake tafiyar da zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari kan tsadar rayuwa

Zanga-zangar 'yan kwadago
Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Majalisar Dokokin Tarayya Saboda Abu 1 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ana sa ran masu zanga-zangar, wadanda ke ta wake-wake za su isar da sakonsu ga shugabannin majalisar dokokin tarayyar, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kwadagon sun yi fatali da gargadi da dama da aka yi masu, sannan suka ci gaba da zanga-zangarsu a kan mawuyacin halin da tattalin arziki ke ciki a kasar.

Wani gargadi DSS ta yi wa 'yan kwadago?

A makon jiya ne hukumar DSS ta yi gargadin cewa wasu mutane na kokarin amfani da damar zanga-zangar da 'yan kwadago suka shirya a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu, domin tayar da zaune tsaye a fadin kasar.

Daraktan hulda da jama'a na hukumar tsaron farin kayan, Dr Peter Afunanya, ne ya yi wannan kira a cikin wata sanarwa da ya saki.

Ya nemi kungiyar kwadago da ta dakatar da zanga-zangar da take nufin yi kan tsadar rayuwa a kasar don samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

‘Yan kwadago sun yanke matsaya kan hakura da zanga-zanga saboda barazanar DSS

Ya bukaci cewa su nemi hanyar sulhu maimakon yin abin da ka iya haifar da tashin hankali a kasar.

Ga bidiyon zanga-zangar a kasa:

'Yan kwadago sun fara zanga-zangar gama gari

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar TUC ta ce ba za ta shiga wannan zanga-zangar ta 'yan kwadago ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel