Yadda DSS Suka Dakile Dakarun Soji Daga Yin Juyin Mulki Zamanin Buhari, FFK Ya Tona Asiri

Yadda DSS Suka Dakile Dakarun Soji Daga Yin Juyin Mulki Zamanin Buhari, FFK Ya Tona Asiri

  • Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufuri, ya ce DSS sun dakile shirin dakarun soji na yin juyin mulki zamanin Shugaba Muhammadu Buhari
  • Jigon jam'iyar APC na aiki tare da wasu hukumomin tsaro wajen yaki da ta'addanci inda ya bada tabbaci kan dorewar dimokuradiyyar Najeriya
  • Fani-Kayode, wanda aka fi kira da FFK, ya bayyana wannan ikirarin nasa yayin kare shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi kan wasu zarge-zarge

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Femi Fani-Kayode, jigon jam'iyyar APC kuma ministan sufurin jiragen sama ya ce hukumar tsaron farin kaya (DSS) a karkashin Yusuf Magaji Bichi ta cancanci yabo.

Ya ce ko a zamanin a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, hukumar DSS ta dakile wani yunkuri na yin juyin mulki, Legit ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NPA v Intel: Dalilin maidawa tsohon kamfanin Atiku kwangila da Tinubu ya hau mulki

Femi Fani Kayode/DSS/Muhammadu Buhari/Soji/Dakaru
Femi Fani Kayode ya yi ikirarin cewa dakarun soji sun so hambarar da gwamnatin Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

Tsohon ministan, yayin nuna kwazon Bichi, ya yi ikirarin cewa shugaban DSS din ya taka rawa wajen dakile shirin wasu dakarun soji daga hambarar da gwamnatin Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fani-Kayode ya kuma jinjinawa kokarin DSS karkashin shugabancin Bichi na yaki da ta'addanci, dakilewa tare da fallasa yunkurin juyin mulki don dorewar dimokuradiyya a kasar.

Ya kamata 'yan Najeriya su jinjinawa shugaban DSS, FFK ya yi bayani

Ya yi kira ga masu kalubalantae shugaban DSS da su kasance masu jinjinawa kokarin Bichi na yaki da cin hanci da rashawa da kuma 'yan ta'adda.

Tsohon ministan ya bayyana hakan lokacin da ya ke kare Bichi da hukumar DSS kan zargin da Jackson Ude, wani dan jarida yake yi wa hukumar na samun nakasu a fuskar sadarwa.

Fani-Kayode ya ce:

"Bari na kara nanatawa, ba don Bichi da DSS ba, da tuni Boko Haram da ISWAP sun mamaye Abuja tun tuni, kuma da wasu dakarun soji sun yi juyin mulki a zamanin Buhari.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sama da 200 sun shirya tsaf don tabbatar da Abba Gida-Gida ya yi nasara a kotu

"Shi tare da hadin guiwar wasu jami'an tsaro suka fallasa wannan yunkuri na wasu bata garin soji na hambarar da gwamnatin Buhari, don tabbatar da dorewar dimokuradiyya."

Kalli jawabin nasa a kasa:

Matar aure ta datse igiyar aurenta na wata 6

A wani labarin, wata mata ta wallafa a shafinta na TikTok dalilin da ya sa ta yanke shawarar datse igiyar aurenta duk da bai wuce wata shida ba.

Matar wacce ba a gano asalin sunanta ba, ta ce ta gaji da fadace-fadacen mijin, inda ta nemi kawarta tazo ta raba ta da gidan, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel