Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Kisa Kan Kashe Jami’an DSS 7 a Shekarar 2015

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Kisa Kan Kashe Jami’an DSS 7 a Shekarar 2015

  • Bayan shekaru takwas wata babbar kotu da ke Ikeja, jihar Legas, ta yanke wa wani hukuncin kisa bisa kama shi da laifin kashe jami'an DSS guda 7
  • Hakazalika, kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari ga wani da aka gabatar gabanta da hannu a kashe jami'an
  • An kashe jami'an ne a yayin da suka je yin bincike kan matar wani dan jarida da aka yi garkuwa da matarsa, inda 'yan bindigar suka budewa jami'an wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ikeja, jihar Legas - Wata babbar kotu da ke Ikeja ta samu wasu mutane biyu da laifin kisan wasu jami’ai bakwai na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Gobara ta yi barna yayin da wuta ta ci hukumar shari’a a jihar Kano

Alkalin kotun, Hakeem Oshodi, ya yankewa Clement Ododomu hukuncin kisa ta hanyar rataya da Tiwei Monday daurin shekaru 16 a gidan yari.

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas
Alkalin kotun, Hakeem Oshodi, ya yankewa Clement Ododomu hukuncin kisa ta hanyar rataya da Tiwei Monday daurin shekaru 16 a gidan yari. Hoto: Federal High Court
Asali: UGC

Laifukan da ake tuhumar wadanda ake zargin sun aikata

Rahoton The Cable ya bayyana cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 14 ga Satumba, 2015, a Ishawo Creek, Ikorodu, Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gurfanar da su ne a kan tuhume-tuhume 10 da ke da alaka da hada baki wajen aikata kisa da kisa da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da ya ci karo da sashe na 223 da 298 (3) na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa hukumar DSS ta samu kiran gaggawa daga wani editan jaridar Sun (an sakaya sunansa) a ranar 14 ga Satumba, 2015, game da sace matarsa ​​da aka yi a gidansu.

Kara karanta wannan

“Kar wanda ya ajiye mun laya a kotu”: An sha dirama yayin da alkali ya yi gargadi da kakkausar murya

Wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifukan

Hukumar DSS ta jihar ta aike da tawagar jami'ai tara domin gano mabuyar masu garkuwa da mutanen inda ‘yan bindigar suka yi wa jami'an kwanton bauna tare da kashe bakwai.

Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin yayin da suka gabatar da cewa sun je Legas ne domin halartar jana’izar kakarsu, The Guardian ta ruwaito.

Amma a hukuncin da aka yanke, Oshodi ya ce wadanda ake karar sun gaza samar da muhimman shaidu don tabbatar da ikirarinsu, tare da cewa wadanda ake tuhumar ba su nuna nadama kan laifukan da suka aikata ba.

DSS ta gurfanar da dan Boko Haram da ya kai hari a masallacin Kano a 2014

A wani labarin, DSS ta sake gurfanar da Husseni Isma'il da ake zargi da hannu a harin bam kan masallacin Kano, kamar yadd Legit Hausa ta ruwaito.

Ana zargin Ismail wanda aka fi sani da Maitangaran da kisa harin kan babban masallacin a shekarar 2014, cewar TheCable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel