Bikin Sallah: DSS ta Shawarci Masallata Yayin da Ake Shirin Fita Sallar Karamar Idi

Bikin Sallah: DSS ta Shawarci Masallata Yayin da Ake Shirin Fita Sallar Karamar Idi

  • Rundunar tsaro ta farin kaya DSS ta bawa masallata shawarwari yayin gudanar da sallar idi ta hanyar ba su bayanan da za su taimaka wajen dakile rashin tsaro
  • Musulmin kasar nan za su fara bukukuwan sallah ƙarama a Larabar nan bayan masu duban wata sun gaza ganin jaririn watan Shawwal
  • DSS ta shawarci musulmi su yi gaggawar kai rahoton duk wani motsin da ba su gamsu da shi ba ga hukumomin tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Rundunar Tsaro ta farin Kaya DSS ta shawarci musulmi da su sanya ido sosai yayin da suka isa filin idi domin gudanar da sallah da za a fara gobe Laraba.

Kara karanta wannan

An Samu Sabani a NNPP Saboda Sabuwar Alamar Jam'iyyar da Kwankwaso ya Kaddamar

Rundunar ta shawarci musulmi da su gaggauta mika duk wasu bayanan motsin da ba su aminta da su ba, kamar yadda rahoton daily trust ya nuna.

'Yan DSS
DSS tayi kira game da shirin karamar sallah
Asali: Twitter

DSS ta ce musulmi su kwantar da hankalinsu, su kuma gudanar da bukukuwan sallah cikin nutsuwa, domin tuni aka samar da matakan kare rayukansu da dukiyoyinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban jami’in hulda da jama’a na rundunar DSS, Peter Afunanya ya bayyana haka yayin da ake shirin shagulgulan sallah karama.

A kalaman Afunanya:

“Muna shawartar kowa ya sa ido sosai tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani mosti da ba su gamsu da shi ba.”
“A bangarenmu, za mu ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da an gudanar da bukukuwan cikin salama.”

Za a gudanar da bikin sallah gobe

Kara karanta wannan

Sauyin yanayi: Tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 za su samu aiki da gwamnatin tarayya

Bayan gaza ganin jaririn watan Shawwal a yammacin Litinin ne dai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ayyana Laraba a matsayin 1 ga watan ƙaramar sallah.

Tun a ranar Lahadi, fadar Sarkin Musulmin ta buƙaci Musulmin Najeriya su fara duban watan Shawwal a yammacin Litinin.

Abubuwan da musulmi ke yi ranar Sallah

Ranar Sallah dai na daga lokutan da aka fi son musulmi su yi kwalliya da tufafi mai kyau, su yawaita kabbara, su je sallar idi sannan su sada zumunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel