EFCC Ta Shiga Runtsi, Kotu Ta Ce Dole a Fito da Emefiele Ko Kuwa a Kyale Shi Ya Tafi Gida

EFCC Ta Shiga Runtsi, Kotu Ta Ce Dole a Fito da Emefiele Ko Kuwa a Kyale Shi Ya Tafi Gida

  • An cigaba da kokarin sauraron shari’ar da ake yi tsakanin lauyan Godwin Emefiele da hukumar EFCC a Najeriya
  • A maimakon jami’an EFCC su gurfanar da tsohon Gwamnan bankin a kotu kamar yadda aka umarta, ba su yi haka ba
  • Kotun tarayya da ke Abuja ta tsaya a kan bakan ta cewa dole a kawo mata Emefiele ko kuwa a kyale shi ya tafi gida

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Alkalin kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, Olukayode Adeniyi, ya jaddada umarnin da ya ba hukumar EFCC a baya.

A ranar Litinin da kotu ta zauna, This Day ta ce Mai shari’a Olukayode Adeniyi ya bukaci EFCC ta gaggauta sakin Mr. Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

Ga mari, ga tsinka jaka: APC ta yi wa Peter Obi raddi kan batun shari’ar zaben 2023

Alkalin ya nanata wannan umarni ne saboda hukumar ta gaza gabatar da tsohon gwamnan bankin na CBN a gaban kotunsa a jiya.

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele a kotu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Godwin Emefiele ya shiga hannu

Idan ba za a kawo shi kotu domin ba shi beli ba, Olukayode Adeniyi ya ce babu dalilin da za a cigaba da tsare Emefiele a fuskar dokar kasa.

Da aka zauna domin cigaba da shari’a a makon nan, jami’an EFCC ba su kawo Emefiele ba wanda ya rike babban banki na shekaru.

Meya hana EFCC ta gurfanar da Emefiele

Rahoton ya ce Lauyan da ya tsayawa hukumar EFCC, Farouk Abdallah, ya ce matsalar takardu ya jawo ba a iya kawo Emefiele ba.

A nan Alkalin ya sake nanatawa kotu cewa wajibi ne sai an bi umarnin da ya bada kafin a iya cigaba da sauraron shari’ar a gabansa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Za Ta Kirkiro Sababbin ‘Yan Sanda Domin Gadin Ma’adanai

Watakila a zo da Emefiele a gobe

Vanguard ta ce Mai shari’a Adeniyi ya kuma umarci lauyan Emefiele watau Mathew Burkaa ya tabbata an tanadi takardun da ake bukata.

Bayan nan ne sai kotu ta dage zama zuwa gobe Laraba, 8 ga watan Nuwamba 2023.

Zuwa gobe ake sa ran Emefiele zai bayyana a kotu inda ya ke kalubalantar cigaba da tsare shi da gwamnatin Najeriya ta ke yi tun a Yuli.

Bashin da ake bin Najeriya ya karu

Bayan Muhammadu Buhari ya damka masa mulki, Bola Tinubu zai ci bashin $7.8bn da €100m, an ji labari hakan zai jawo bashi ya karu.

Sakamakon karya darajar Naira da N300 a kan Dala 1, alkaluma sun nuna zuwa karshen 2023 zai zama ana bin Naeriya bashin 89.2tr.

Asali: Legit.ng

Online view pixel