Kungiyar Ƙwadago Ta Yi Wa Hukumar DSS Martani Mai Zafi Kan Yunkurin Hana Ta Yin Zanga-Zaga

Kungiyar Ƙwadago Ta Yi Wa Hukumar DSS Martani Mai Zafi Kan Yunkurin Hana Ta Yin Zanga-Zaga

  • Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun yi wa hukumar DSS martani bayan ta nemi kungiyoyin su hakura da zanga-zangar da suka shirya yi
  • Hukumar DSS ta ce ta gano cewa akwai wasu bata gari da ke shirin amfani da zanga-zangar wajen tayar da zaune tsaye a kasar
  • Sai dai shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya ce kungiyoyin ba za su karbi uzurin DSS ba, saboda zanga-zagar lumana ce za su gudanar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugabannin kungiyoyin ƙwadago sun yi wa hukumar tsaron farin kaya (DSS) martani kan yunkurin hana ta gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya.

A ranar Laraba ne shugabannin kwadago suka ce ba gudu ba ja da baya daga kudirin da suka yi na gudanar da zanga-zanga a ranar 27 da 28 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

NLC ta yi wa DSS martani
Kungiyar kwadago ta magantu kan yunkurin DSS na hana ta gudanar da zanga-zanga. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

NLC da TUC sun zargi DSS da yunkurin yi masu barazana

Tun da fari hukumar DSS ta gargadi kungiyar kwadago ta NLC da TUC da su kauracewa yin zanga-zagar saboda wanzar da zaman lafiya a fadin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai da ya ke martani kan wannan gargadi na DSS, Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC na kasa ya ce maimakon yi wa kungiyar barazana, kamata ya yi DSS ta kama wadanda take zargi.

Ajaero ya ce tarihi ba zai taba yafewa ƙungiyar ƙwadago ba ma damar ta zauna ta yi shiru alhalin 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ba, rahoton Daily Trust.

Kungiyoyin kwadago ba za su hakura da zanga-zanga ba

Shugaban kungiyar kwadagon ya ce:

"Za mu yi zanta zangar ne cikin lumana don adawa da tsadar rayuwa. Kungiyar kwadago ba za ta ci gaba da zura idanuwa 'yan Najeriya na shan wahala ba.

Kara karanta wannan

Jami’an EFCC sun kai samame wurin ‘yan canji a Kano, Abuja da Oyo akan wani dalili 1 tak

"Muna so hukumar DSS ta sani cewa babu inda aka taba samun tashin hankula a zanga-zagar lumana da kungiyar ta taba gudanarwa, don haka batun mu janye bai taso ba."

Shugaban NLC ya koka kan yadda tattalin arzikin kasar ya tabarbare inda ya ce yanzu haka darajar dala ta kai N1,900.

Ya ba da tabbacin cewa babu wanda ya ke son cigaban Najeriya kamar kungiyar kwadago kuma ba za ta taba yin wani abu da zai jawo rashin zaman lafiya ba.

Shugaba Tinubu ya nada sabuwar shugabar hukumar 'immigration'

A yammacin yau Laraba ne Legit Hausa ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya amince da nadin DCG Kemi Nansap a matsayin sabuwar shugabar hukumar shige da fice ta kasa (NIS).

Nadin na ta wanda zai fara aiki a ranar 1 ga watan Maris, 2024 ya biyo bayan karewar wa'adin shugabar hukumar ta yanzu Misis Caroline Wura-Ola Adepoju.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Cif Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel