Hukuma Ta Cafke Tsohon Shugaban NIRSAL Bayan Watanni Ana Binciken Zargin Satar N5bn

Hukuma Ta Cafke Tsohon Shugaban NIRSAL Bayan Watanni Ana Binciken Zargin Satar N5bn

  • Rahoto mai karfi ya tabbatar da tsohon shugaban hukumar NIRSAL ya na hannun jami’an tsaro a halin yanzu
  • An dade ana zargin Aliyu Abdulhameed da satar dukiyar gwamnati, yanzu an yi ram da shi domin yin cikakken bincike
  • Tun a karshen 2022 aka sauke Abdulhameed daga kujerar da yake kai a NIRSAL bayan zargin handamar kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kusan shekara guda kenan bayan an kori Aliyu Abdulhameed daga matsayin shugaban hukumar NIRSAL, a yanzu ya shiga hannu.

Rahoto na musamman ya fito daga Daily Trust cewa an yi ram da Aliyu Abdulhameed, ana zagi ya tafi da motoci akalla 32 na ofis.

NIRSAL's Aliyu Abdulhameed
Tsohon Shugaban NIRSAL, Aliyu Abdulhameed Hoto: @woye1
Asali: Twitter

Zargin da ke kan Aliyu Abdulhameed a NIRSAL

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Atoni Janar na Kano Dederi ya shiga matsala, an nemi a hukunta shi

Zargin satar wasu kudi da su ka hada da N5.6bn na kwangilar noma alkama a Kano da Jigawa a 2018 su ka jawo aka kori Aliyu Abdulhameed.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane fiye da 20, 000 aka sa rai wannan tsari zai taimakawa, amma a karshe ana zargin shugaban na NIRSAL ya sulale da biliyoyin kudin aikin.

Abdulhameed da kamfanonin da aka ba kwangilar sun karyata zargin da ake yi masu. Har yau babu iri, taki da sauran kayan noman alkalaman.

Buhari ya kori Abdulhameed daga NIRSAL

A Disamban shekarar bara watau 2022, shugabannin CBN su ka bada shawarar a kori Abdulhameed, sai Muhammadu Buhari kuma ya amince.

Kamar yadda aka sani hukumar NIRSAL ta na karkashin kula da sa idon babban bankin CBN, hakan ya jefa tsohon shugaban a matsala.

Yadda aka kama tsohon shugaban NIRSAL

Kara karanta wannan

Ganduje ya karya Ministan Buhari, an bar Wike ya samu yadda yake so a jam’iyyar APC

Rahoton ya ce a karshen makon jiya ne aka cafke Abdulhameed a harabar wata ma’aikata, inda ya je yana kamun kafa a dawo da shi ofis.

Majiyar ta ce an yi ta aika masa gayyata amma bai halarta ba, sai a makon jiya aka damke shi wajen neman mukami a gwamnatin tarayya.

Tinubu ya shiga bincike na musamman a CBN

Bayan hawan Bola Ahmed Tinubu mulki a watan Mayu, sai ya dauko Jim Obazee domin ya yi bincike a kan abubuwan da su ka faru a CBN.

Kafin a cafke tsohon shugaban na NIRSAL, jami’an DSS, ‘yan sanda da kuma mutanen Obazee sun shafe watanni biyar suna neman shi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel