Kasar Yarbawa: Yadda Buhari Ya Tura DSS Don Su Kashe Ni, Sunday Igboho Ya Yi Zargi

Kasar Yarbawa: Yadda Buhari Ya Tura DSS Don Su Kashe Ni, Sunday Igboho Ya Yi Zargi

  • Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, ya dawo Najeriya karo na farko a cikin shekaru uku
  • Dan gwagwarmaya Igboho ya sa kafar wando daya da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda rikicin makiyaya da manoma a Kudu maso Yamma
  • Igboho, wanda ya dawo bikin mutuwar mahaifiyarsa, ya yi zargin cewa tsohon Shugaban kasa Buhari ya yi kokarin kashe shi a lokacin da yake fafutukar kasar Yarbawa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Saki, jihar - Dan gwagwarmayar kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, ya yi zargin cewa tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura jami'an DSS domin su kashe shi.

Igboho ya bayyana a ranar Juma'a, 23 ga watan Fabrairu, cewa ya dawo Najeriya ne yana mai imani da samun kariyar Ubangiji.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ta ce ainahin mijinta ya rasu a 2017? Gaskiya ta bayyana

Igboho ya bayyana yadda Buhari ya so hallaka shi
Kasar Yarbawa: Yadda Buhari Ya Tura DSS Don Su Kashe Ni, Sunday Igboho Ya Yi Zargi Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, 'dan gwagwarmayar ya dawo Najeriya ne a ranar Alhamis, domin binne mahaifiyarsa a yankin Saki na jihar Oyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga magoya bayansa a jihar Oyo cikin harshen Yarbanci, ya yi zargin cewa fafutukar da yake yi kan rikicin Fulani makiyaya da suka addabi manoma a Kudu maso Yamma shine dalilin da yasa aka yi yunkurin kashe shi.

Ya ce:

"Buhari ya tura sojojinsa da DSS domin su kama ni a gidana saboda na ce Yarbawa ba bayin Fulani bane, ba za su tauye mu a kasar iyaye da kakanninmu ba.
"Fulani ba za su hana iyayenmu maza da mata zuwa gonakinsu ba. Amma, na dawo da karfin ikon Allah amma ba na mutum ba."

Gwagwarmayar Igboho a gwamnatin Buhari

Kara karanta wannan

Gawarwaki sun fara rubewa a barikin soja bayan matakin da kamfanin wuta ya dauka, an fadi dalili

A 2021, bayan wani rikici da ya barke tsakanin abokansa da jami’an DSS a gidansa da ke Ibadan a Najeriya, Sunday Igboho, mai fafutukar neman ‘yancin Yarabawa ya bar Najeriya.

Ya nemi mafaka a Jamhuriyar Benin bayan da hukumar DSS ta ayyana nemansa ruwa a jallo.

A watan Oktoban 2021, an kama shi a Jamhuriyar Benin yayin da yake yunkurin tafiya Jamus.

Ya sha tuhume-tuhume a wannan kasar kan zargin hada baki da wasu masu aikata laifuka.

Shehu Sani ya caccaki malamin da ya nemi a kashe matar Tinubu

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi martani bayan wani malamin addinin Musulunci ya ayyana cewa matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta cancanci mutuwa saboda kasancewarta fasto.

Sani ya yi Allah wadai da furucin malamin sannan ya jaddada cewar 'yan kasa na da 'yancin sukar gwamnati da manufofinta, amma neman mutuwar matar shugaban kasar ba abun yarda bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel