Hukumar DSS Ta Kama Aisha Yesufu? Gaskiya Ta Bayyana

Hukumar DSS Ta Kama Aisha Yesufu? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wani rubutu da aka yi a dandalin Facebook a 2024 ya yi ikirarin cewa rundunar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama Aisha Yesufu
  • Jaridar Legit ta rahoto cewa Yesufu, wacce ta kasance ta hannun damar Peter Obi, tana yawan caccakar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC mai mulki
  • Wani dandalin binciken kwakwaf ya nemo hujja da zai marawa ikirarin da aka yi na zargin kama Yesufu baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

FCT, Abuja - Wani rahoto da aka wallafa a ranar 18 ga watan Fabrairu, ya yi ikirarin cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama Aisha Yesufu.

Yesufu ta kasance babbar mai sukar gwamnatin jam'iyyar APC kuma ta hannun damar Peter Obi, 'dan takarar jam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dura kan 'yan Crypto, ta kakaba wa Binance tarar dala biliyan 10

An gano gaskiya kan batun kama Aisha Yesufu
Hukumar DSS Ta Kama Aisha Yesufu? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Patrick Meinhardt/Aisha Yesufu
Asali: UGC

Mawallafin labarin ya yi ikirarin cewa an kama Yesufu ne saboda dagewa da ta yi cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ba halastaccen shugaban kasa bane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana iya samun ikirarin a nan da nan.

Rubutun na cewa:

"Yanzun nan: DSS ta kama Aisha Yesufu bisa umurnin Tinubu kan kalaman rashin adalci kan Shugaban kasar.
"Yanzun nan DSS ta kama mai watsa shirye-shirye Aisha Yesufu kan kin daukar Tinubu a matsayin shugaban kasarta da kuma ikirarin cewa magudi ne ya kai shugaban kasar ofis."

Menene gaskiya game da ikirarin kama Aisha Yesufu?

Bayan wannan ikirari, wani dandalin binciken gaskiya, Africa Check, ya yi bincike a kai.

Bayan bincikensa, dandalin ya yanke hukuncin cewa babu wata hujja da ke nuna cewa an kama Yesufu.

Ya ce idan aka yi la’akari da shaharar Yesufu, da wuya jami’an DSS su ka kama ta ba tare da kafafen yada labarai sun kawo rahoton ba. Babu irin wannan rahoto daga ingantattun kafafen yada labarai.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Abba ya soki aikin Hisbah a Kano

A wani labari na daban, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yana ganin akwai kura-kurai a yadda wasu hukumomi suke gudanar da aikinsu.

Gidan rediyon Freedom ta rahoto Mai girma Abba Kabir Yusuf yana kokawa kan yadda jami’ai kan ci zarafin wadanda ake zarfi da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel