Muhammadu Buhari
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yayi Allah wadai da kisan ɗan takarar sanata na jam'iyyar Labour Party, Cif Oyibo Chukwu, a Enugu ta Gaɓas ana dab da zaɓe.
A ranar Alhamis ne Buhari ya dura jihar Katsina domin yin zaben shugaban kasa na ranar Asabar na shugaban kasa da 'yan majaisun tarayya a zaben 2023 na bana.
Abubakar Malami, Antoni Janar kuma ministan shari'a ya ce gwamnatin tarayya ba ta saba umurnin kotun koli ba kan batun wa'adin dena amfani da tsaffin naira.
Shugaban jam'iyyar, APC, na kasa, Abdullahi Adamu ya karyata cewa akwai wasu masu yin zagon kasa a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ake kira 'cabal'.
Muna Bawa Yan Najeriya Hakuri Abisa Zaben da Muka saka Sukayi Na APC, Mun fita Daga Tafiyar, Zuwa PDP ta Atiku Abubakar Da Okowa - CewarKungiyar Magoya Baya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan takarar da za su fafata a dukkan matakai da su garzaya kotu idan basu gamsu da sakamakon zaben hukumar INEC ba.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki masu neman zama shugaban kasa, gwamna, da sauran mukaman siyasa su amince da duk abinda INEC ta sanar bayan zaɓe .
Za a ji wasu Kungiyoyin Magoya Bayan Buhari/Osinbajo su na goyon bayan Atiku Abubakar. A zaben da za ayi, kungiyar ta ce tana harin nasarar Atiku/Okowa a 2023.
Yan kwanaki kafin zabe, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu.
Muhammadu Buhari
Samu kari