Magana ta Kare: Ministan Buhari Ya Fadawa Tinubu Ya Tsara Jawabin Zama Shugaban Kasa

Magana ta Kare: Ministan Buhari Ya Fadawa Tinubu Ya Tsara Jawabin Zama Shugaban Kasa

  • Ministan harkokin jirgin sama a Najeriya ya ba Jam’iyyar APC da Bola Tinubu nasara
  • Ko da ba a kammala tattara kuri’un zaben 2023 ba, Hadi Sirika ya na sa ran sun yi galaba
  • Sanata Sirika ya fadawa Tinubu ya yi azamar rubuta jawabi a matsayin wanda ya lashe zabe

FCT, Abuja - Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika ya nuna Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa zai lashe zaben 2023.

Hadi Sirika da yake magana a shafin Twitter a ranar Litinin, ya fadawa Asiwaju Bola Tinubu ya rubuta jawabin lashe zaben shugaban kasa.

The Cable ta ce Ministan ya bukaci ‘dan takaran na APC ya rubuta gajeren jawabi ta yadda magoya bayansa za su iya barci da kyau da dare.

Ministan tarayyar yana ganin kamar ‘dan takaran ya lashe zaben sabon shugaban kasa, ya gaji kujerar Mai girma Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Caccaki Jam’iyya, Ya Jero Abin da Ya Jawo Masu Rashin Nasara

Sirika ya kokari wajen kawowa jam’iyyar APC nasara a rumfarsa da mazabarsa a jihar Katsina.

Asiwaju da Tinubu
Asiwaju da Tinubu ana dariya Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hankali kwance

“Duk da fushin abin da ya faru a Legas, Osun, Kano, Katsina, Yobe, Gombe da wasu jihohin, ‘Shugaba mai jiran-gado’, Bola Ahmed Tinubu ya fara rubuta jawabin samun nasara a yanzu.
Amma Mai girma, ka rubuta gajeren jawabi, za mu yi barci da wuri a yau. ‘Babu tashin hankali’ Godiya ta tabbata ga Allah.”

'Yan adawa su na neman yin bore

Ministan ya yi wannan magana ne a lokacin da ake tattara sakamakon zaben sabon shugaban kasar, zuwa yanzu ba a san wanda ya yi nasara ba.

Can kuma aka ji 'dan siyasar yana cewa Asiwaju ya lashe zabe tuni. #Jagaban2027

Ganin hayaniyar da aka yi wajen tara kuri’u, Sirika ya ce babu yadda Emeka Ehidioha suka iya da Femi Fani-Kayode, Dele Alake, da Festus Keyamo.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

Da yake magana a shafin na sa, Ministan ya ce duk surutun wakilan PDP a wajen tara kuri’u, sai da su hakura da mutanen da jam’iyyarsa ta aika.

A wata maganar da ya yi, tsohon ‘dan majalisar ya ce a zabukan 2003, 2007, 2011 zuwa 2015, yana cikin wakilan Muhammadu Buhari na kasa.

Duk da zargin magudi da ake yi a lokacin, Sirika ya ce bai taba ficewa daga dakin tara kuri'u ba, yana mai ba masu kuka shawarar su kai kara a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel