Daga Karbar Satifiket a Hannun INEC, Tinubu Ya Garzaya Daura Domin Ganawa da Buhari

Daga Karbar Satifiket a Hannun INEC, Tinubu Ya Garzaya Daura Domin Ganawa da Buhari

  • Da yammacin nan aka ga hotunan ganawar Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Muhammadu Buhari
  • Zababben Shugaban Kasar ya ziyarci garin Daura a Jihar Katsina domin zama da wanda zai gada
  • Kashim Shettima da Sanata Abdullahi Adamu na cikin ‘yan tawagar shugaban kasan mai jiran-gado

Katsina - A yammacin Laraba, 1 ga watan Maris 2022, Bola Ahmed Tinubu ya hadu da Mai girma Muhammadu Buhari a garin Daura.

Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai, Buhari Sallau ya wallafa hotunan haduwar mai gidansa da mai jiran gado.

Buhari Sallau ya ce Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Bola Ahmed Tinubu da abokin gaminsa watau Sanata Kashim Shettima.

An yi wannan zama a gidan shugaban kasar da ke Daura a jihar Katsina. Tun lokacin zaben shugaban kasa, Buhari ya tare a mahaifarsa.

Kara karanta wannan

"Shi Ne Daidai" Gwamna Masari Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe

Jirgi ya sauka a Katsina

Jaridar Aminiya ta ce zababben Shugaban Kasar ya sauka filin jirgin sama na Ummaru Musa Yar’adua a Katsina tare da kusoshin APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta lura, tawagar shugaban kasan mai jiran gado ta hada da Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Nasir El-Rufai.

Tinubu Daura
Tinubu da Buhari a Daura Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Sannan akwai Gwamnoni masu-ci; Bello Matawalle, Badaru Abubakar, Abubakar Sani Bello da tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.

Rahoton ya ce a tawagar akwai Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari da mataimakinsa, Mannir Yakubu da mukarrabansu su ka tarbi ayarin a kan hanyar zuwa Daura.

Da yake bayani a Twitter, shugaban na Najeriya ya tabbatar da wannan zama a yau, inda ya shaida satifiket din wadanda suka lashe zaben bana.

"Ina mai farin cikin karbar bakuncin Mai girma zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Mai girma Kashim Shettima a gida na a Daura a yau.

Kara karanta wannan

Masari Ya Shiga Sallamar Masu Rike da Mukamai Tun da Aka Kunyata Tinubu a Katsina

Mutum biyu da suka yi imani da Najeriya kuma suke kokarin kawo cigaba da samun karuwa.”

- Muhammadu Buhari

Tinubu: Barka! Barka! - Buhari

Kamar yadda labari ya zo da safiyar nan, Shugaban Najeriya ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben sabon shugaban kasa da aka yi a makon jiya.

Malam Garba Shehu ne ya fitar da jawabi a madadin Muhammadu Buhari bayan nasarar APC, ya ce Tinubu ya fi kowa cancanta a jerin masu takaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel