Yan Kungiyar Buhari-Osinbajo Tun 2019 Sunyi Fatali Da Tafiyar Sun Nemi Yafiyar Yan Najeriya

Yan Kungiyar Buhari-Osinbajo Tun 2019 Sunyi Fatali Da Tafiyar Sun Nemi Yafiyar Yan Najeriya

  • Kungiyar yakin neman zaben Buhari-Osinabanjo a 2019 Tayi Nadamar Saka Yan Najeriya Zabar Buhari da Osinbajo a Shekarun Baya
  • Kungiyar ita da Magoya Bayanta Kimanin Miliyan Tara Sun Bukaci Yan Kasa Su Yafe Musu
  • Yayin da Daukacin Mambobin Kungiyar Suka Sauya Sheka PDP nan Take

Abuja- Wata Kungiya da tayi fafutukar ganin Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Osinbajo ta hau karagar mulki a shekarar 2019 ta ayyana nadamar ta tare da neman yafiyar yan Najeriya abisa abinda ta kira na tunzura su nuna soyayya makuniya.

Kungiyar mai suna "Buhari-Osinbajo Support Groups" na rajin marawa tafiyar Muhammadu Buhari baya ne kafin zuwa wannan lokaci, amma yanzu tuni ta canja salo.

Tana rokon yan Najeriya akan su yafe musu bisa cinikin dare da suka sanya su sukayi ta hanyar nunawa tafiyar APC makauniyar soyayya a 2019.

Kara karanta wannan

Zaɓukan 2023: Kimanin N500bn ne Aka Tanada DOn Sayen Kuri'u, Shugaban EFCC Bawa

Bugu da kari tayi kira ga yan Najeriya wajen kara hakuri abisa halin da ake ciki na rashin jin dadin rayuwa da mulkin ya haifar.

atikuokowa
Dan takarar jamiyyar PDP na Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar Asalin Hoto: Vanguardngr
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na zuwa ne a wani saƙo da kungiyar ta sanar ta hadaka, wadda ta tabbatar da cewa ta ajiye tafiyar jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP domin marawa tafiya Atiku Abubakar da Okowa baya.

Danjuma Fachiwe Gwoza shine shugaban ƙungiyar daya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ƙungiyar ta kira ranar larabar nan a Abuja wanda Jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar sa:

"Daga rana mai kama ta yau, ɗaukacin mambobin wannan ƙungiya tamu ta magoya bayan Buhari da Osinbajo na ƙasa gabaki daya, muna sanar da canja suna da komai namu zuwa Ƙungiyar Magoya Bayan Atiku/Okowa.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Malaman Kano Sun Bayyana Dan Takarar Da Za Su Zaba Tsakanin Atiku Da Tinubu

A cikin batun da Fachiwe Gwoza ya fada, ya tabbatar da cewa kungiyar su tana da magoya baya kimanin miliyan tara a cikin kasar nan, a cewar sa:

....... mambobin mu zasu kai kimanin miliyan Tara da Dubu Ɗari Uku da Dubu Sha Uku da Ɗari Takwas da Arba'in da Shida.

Fachiwe Gwoza yace hakika sunyi nadamar kasancewa magoya bayan jamiyyar APC a shekarun da suka shude, inda yace ba komai bane face sharrin makauniyar soyayya da ta lullube masu idanu.

Ya ƙara da cewa:

"Wannan rashin dace da mukayi, ya jefa ƙasa gabaki ɗaya cikin hali maras kyau.

Fachiwe Gwoza ya godewa jiga jigai a tafiyar kungiyar tasu ta Senator Abubakar Mahdi da Raymond Dokpesi, riwayar AriseNews.

Sannan yayi kira ga yan Najeriya musamman ma yan kungiyar da suyi aiki tukuru wajen ganin sun fatattaki abinda ya kira da jam'iyyar mai bakin kashi, watau APC.

Kara karanta wannan

"Ka Janye Wa Kwankwaso", Wasu Kungiyoyi Suka Roki Atiku Kwanaki Kadan Kafin Zabe

Har ila yau ya kuma kara tabbarwa da mambobin kungiyar da yan Najeriya cewa, zasuyi amfani da mambobin su dake cikin jihohi 36 na kowacce karamar hukuma ta kasa domin ganin nasarar Atiku da Okowa a zabukan 2023.

Bai gushe anan ba yace, zasu bawa mambobin su horo a ayyukan zabe , don ganin PDP tayi nasarar kuri'u mafiya rinjaye a cikin 93,454,008 da za'a kada a Najeriya.

A cewar sa, ƙungiyar yanzu haka ta duƙufa ka'in da na'in don ganin ta tattara adadin kuri'un mafi rinjaye a ko wacce akwati dake cikin ƙasar nan.

Daga karshe yace tunda dokar zabe ta 2022 da aka canjawa fasali ta bada damar tura sakamakon zabe na kai tsaye, zasu yi amfani da kimiyya da fasaha tare da mambobin su wajen tabbatar da narar Atiku da Okowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel