Arewa
Wani abin fashewa ya fashe a jihar Sokoto, wanda ya janyo asarar rayukan mutum huɗu yayin da wasu da dama suka jikkata. Lamarin ya auku ne a shagon mai walda.
Shahaharriyar mai tiƙar rawa a TikTok, Hafsat Fagge wacce aka fi sani Hafsat Baby, ta bayyana cewa yanzu ta tuba kuma a shirye ta ke ta auri kwamandan Hisbah.
Wani mummunan hatsarin mota ya auku kan titin hanyar Lokoja-Abuja. Hatsarin ya auku ne a tsakanin wata motar tanka, ɗauke da man fetur da sauran wasu motoci.
Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji mai kokarin dawo da zaman lafiya a Arewa ta Yamma sun halaka yan bindigan jeji da yawa a yankin Shinkafi, jihar Zamfara.
Wata matar aure ta aikata wata mummunar aika-aika, akan wata ƙaramar yarinya a jihar Kano. Matar auren ta yi yunƙurin halaka ta ne saboda tsananin kishin ta.
Gwamnati a jihar Filato ta yanke sanya dokar kulle ta awanni 24 a yankin ƙaramar hukumar Mangu, jihar Filato bayan kisan rayuka akalla 20 a garuruwa biyu .
Yayin da ake ci gaba da takaddama kan shiyyar da zata jagoranci majalisar tarayya ta 10, manyan arewa sun zauna a Kaduna, sun ce arewa kaɗai zata karbi ragama.
Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya kaddamar aikin gina rukunin gidaje wansa har zuwa watan Mayu, 2023, ba'a kammala gina su ba, tun 2017 aka fara aikin.
Tajuddeen Abbas ya yi bayanin abin da ya sa Arewa maso Yamma ta samu Shugaban majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa a lissafinsu na APC.
Arewa
Samu kari