Abba Gida Gida Ya Yi Shirin Sake Gina Shataletalen Tarihi Da Ya Rusa Zuwa Wani Wuri

Abba Gida Gida Ya Yi Shirin Sake Gina Shataletalen Tarihi Da Ya Rusa Zuwa Wani Wuri

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin sake gina shatatalen nan mai dogon tarihi a wani wuri mafi tsaro da dacewa
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf shi ya tabbatar da haka a ganawarsa da Hana Kaltume wacce ta kirkiri shataletalen tun farko
  • Jama'a sun yi ta korafe-korafe tun bayan rusa wannan shataletale mai dogon tarihi da ke kusa da gidan gwamnatin jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamantin jihar Kano ta bayyana shirinta na sake gina shataletalen da ta rusa da ke kusa da gidan gwamnati a wani wuri na daban.

Gwamnatin ta ce zata sake gina shi a kusa da gadar sama ta Na'ibawa da ke wajen garin Kano wanda ya kasance mafi tsaro.

Abba Gida Gida ya yi alkawarin sake gina shataletalen da ya rusa a Kano
Shataletale Mai Dogon Tarihi Da Abba Gida Gida Ya Rusa. Hoto: Channels TV.
Asali: Twitter

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf shi ya bayyana haka yayin ganawa da Kaltume Hana wacce ta kirkiri shatatalen inda ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin kawo abubuwan ci gaba a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Dubban Matasa Sun Fito Zanga-Zanga Kan Rusau Da Gwamnatin Abba Gida Gida Ke Yi

Abba Gida Gida ya yi alkawarin sake gina shataletalen a Kano

Abba Gida Gida ya tabbatar wa 'yan jihar cewa ya samo wurin da ya dace a sake gina shatatalen ba tare da kawo wata matsala ba, cewar gidan talabijin na Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Wannan shirin sauya wurin gina shataletalen nan ya nuna yadda muka zaku don ganin mun adana abubuwan da suka shafi al'adunmu a jihar, Muna son samar da ayyuka masu inganci ga mutanen mu."

Hanna Kaltume ana ta bangaren, ta nuna jin dadinta yadda gwamnan ke son ganin ya adana wannan hikima nata da ta samar a jihar.

Gwamnatin jihar tun farko ta rusa shataletalen ne saboda ganin yadda aka gina shi kusa da gidan gwamnati da gwamnan ke ganin zai iya kawo cikas ga tsaro.

A cewarta:

"Ina matukar godiya ga Gwamna Yusuf da gwamnatin jihar yadda suka mutunta aikin da na yi, abin alfahari ne a gare ni yadda za a sake gina shi a wani wuri na daban."

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Siyar Da Filin Da Aka Sanya Cikin Wadanda Za a Rusa, Rimingado Ya Magantu

Abba Gida Gida ya bayyana himmatuwarsa na kawo ayyukan ci gaba

Gwamnatin tana son ganin ta ci gaba da adana al'adun Kano shiyasa ma ta ke kokarin sake gina shataletalen a wurin da yafi tsaro da kuma dacewa.

Kakakin gwamnan jihar, Hisham Habib ya tabbatar da hakan ga 'yan jaridu a cikin wata sanarwa, cewar Punch.

Ya ce:

"Gwamnatin jihar Kano ta himmatu wurin kawo ayyukan ci gaba da kuma adana al'adunmu na wannan yanki.
"Sake gina wannan shataletalen ya tabbatar da irin mutunta al'adu da gwamnatin ke yi a jihar."

Dubban Matasa Sun Fito Zanga-Zanga Kan Rusau Da Gwamna Abba Gida Gida Ke Yi A Kano

A wani labarin, dubban matasa ne suka fito zanga-zangar kin jinin rushe-rushe da gwamnatin Kano ke yi.

Matasan sun taru a otal na Daula wanda aka rusa a kwanakin baya don nuna rashin jin dadinsu.

Gwamna Abba Kabir ya sha alwashin ci gaba da rushe-rushe kan gine-gine da aka gina ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel