Hukumar Wutar Lantarkin Abuja Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Karin Kudin Wuta A Watan Yuli

Hukumar Wutar Lantarkin Abuja Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Karin Kudin Wuta A Watan Yuli

  • Hukumar samar da wutar lanatarki ta AEDC ta karyata cewa tana shirin karin kudi saboda tashin dala.
  • Hukumar ta ce babu wani shiri na karin ganin yadda al'umma ake fama matsin tattalin arziki a yanzu
  • Ta yi alkawarin inganta samar da wutar a yankin Abuja fiye da yadda ake samu don inganta harkar wutar

FCT, Abuja - Hukumar Wutar Lantarki a Abuja (AEDC) ta karya jita-jitar da ake yadawa cewa tana kokarin kudin wuta a watan Yuli mai kamawa.

Hukumar ta bayyana haka ne a Abuja cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin 26 ga watan Yuni.

Hukumar wutar lantarki ta karyata jita-jitar kara kudin wuta
Hukumar Wutar Lantarki, AEDC. Hoto: Leadership.
Asali: Facebook

AEDC ta roki jama'a da su yi fatali da wannan jita-jita cewa ta na kokarin kara kudin wuta yayin da tabbatar cewa babu wannan bayani nan kusa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Karfin Hukumar FRSC Na Kwace Mota Da Cin Tarar Masu Laifi

Hukumar AEDC ta ce babu batun karin kudin wutar a halin yanzu

Hukumar ta roki mutane su yi watsi da rahoton kan karin kudin wutar lantarkin da ake yadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar:

"Muna rokonku da kuyi watsi da wannan jita-jita da ke yawo cewa za a kara kudin wutar lantarki. Ku sani cewa babu wani shiri na karin kudin wuta.
"Muna ba da hakuri kan irin matsalar da hakan zai jawo ga al'umma.

Hukumar a baya cikin wata sanarwa ta bayyana cewa za ta kara kudin wutar lantarki a ranar 1 ga watan Yuli.

A baya hukumar ta sanar da karin kudin wutar kan tashin dala

A cewar sanarwar, karin bai rasa nasaba da yanayin sauyi da aka samu a hada-hadar cinikayya musamman na dala a kasar, cewar Tribune.

A cewar sanarwar:

"Daga ranar 1 ga watan Yuli na 2023, ku sani cewa zamu kara kudin wutar lantarki saboda tashin dala a kasuwanni.

Kara karanta wannan

AEDC: Kamfani Ya Sanar da Sabon Farashi da Lokacin Ƙara Kuɗin Lantarki a Garuruwa 4

"A karkashin tsari na MYTO na 2022, hada-hadar dala bai wuce N441 amma yanzu ya kai N750 wanda hakan yake da tasiri akan yawan wutar da kwastomomi ke sha."

A cikin sanarwar hukumar har ila yau, ta shawarci masu amfani da mitar kati da su sayi wutar da yawa kafin karshen watan Yuni saboda samun damar amfani da wutar kafin sabon karin farashin.

NLC Ta Nuna Kin Amincewarta Kan Karin Kudin Lantarki A Najeriya

A wani labarin, Kungiyar NLC ta yi fatali da shirin kara kudin wutar lantarki a kasar.

Kungiyar ta ce yin hakan a wannan lokaci bai kamata ba duba da yanayin da mutane ke ciki.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi bayyana haka inda yace hakan rashin mutunta kwastomomi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel