Arewa
Daga karshe dai an yi wa marigayi magajin garin Zazzau gatan da ake wa kowane Musulmi idan kwanansa ya ƙare, an masa Sallah kuma an kai shi makwanci.
Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina ya bukaci bai wa mutane damar siyan bindiga a kasuwa don kare kansu kamar yadda 'yan bindiga ke yi a kasuwanni.
Gwamna Abba Kabir da Sanata Rabiu Kwankwaso sun gwangwaje dalibai da makudan daloli har 200 kafin tashinsu zuwa kasar Indiya don karo karatun digiri na biyu.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake daukar nauyin dalibai 1001 zuwa kasashen waje don karo karatu, daliban za su fara tashi a yau Juma'a.
Wasu tsagerun 'yan bindiga da ake kyautata zaton yan daban siyasa ne sun farmaki ayarin ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar jam'iyyar SDP, Yakubu Ajaka.
Shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Plateau na zargin jami'an sojoji a jihar da sace shugaban jam'iyyar da ke yankin Jos ta Kudu, Mista Dung Tari a yankin.
Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wani matashi kan zargin yunkurin kisan wani almajiri don daukar fansa kan malaminsu da ya hana shi aure.
Akalla tubabbun mayakan Boko Haram dubu 6,900 ne su ka samu 'yancin shigo wa cikin al'umma a jihar Borno bayan gwamnatin jihar ta gama tantance su.
Wani mummunan hatsari da ya auku a kan hanyar zuwa Potiskum ta jihar Yobe ya yi ajalin aƙalla mutane 38 yayin da wasu sama da 40 ke kwance a Asibiti.
Arewa
Samu kari