Abba Gida Gida da Kwankwaso Sun Raba Wa Dalibai Dala 200 Kafin Tashi Zuwa Indiya

Abba Gida Gida da Kwankwaso Sun Raba Wa Dalibai Dala 200 Kafin Tashi Zuwa Indiya

  • Yayin da dalibai ke shirin tafiya kasar Indiya don karo karatu, Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir sun yi musu goma ta arziki
  • A cikin wani faifan bidiyo, an gano Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir na rabon Daloli ga daliban a cikin jirgi yayin tashi zuwa kasar Indiya
  • Gwamnatin jihar Kano a jiya Alhamis ta kaddamar da shirin daukar nauyin dalibai zuwa kasashen Indiya da Uganda don karo karatun digiri na biyu

Jihar Kano – An gano Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso na raba wa dalibai Daloli a cikin jirgi.

Abba da Kwankwaso na raba Dalolin haR 200 ga daliban da gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen Indiya da Uganda.

Abba da Kwankwaso na raba Daloli ga dalibai a jirgi
Abba Gida Gida da Kwankwaso Sun Raba Wa Dalibai Daloli. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Meye Abba da Kwankwaso ke yi wa daliban Kano?

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban Karamar Hukuma da Wasu Mutane 12 a Jihar Arewa

A cikin wani faifan bidiyo, an gano Abba da Kwankwaso a cikin jirgi suna rabiyar kudaden ga dalibai daf da tashinsu zuwa kasar Indiya don karo karatun digiri na biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rabon kudaden ya faru ne filin tashi da saukan jirage na Aminu Kano a safiyar yau Juma’a 20 ga watan Oktoba yayin da su ke shirin barin kasar.

A jiya Alhamis, 19 ga watan Oktoba ne Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da shirin daukar nauyin daliban zuwa Jami’o’in kasashen Indiya da Uganda don samun damar karo karatu.

Meye Abba da Kwamkwaso ke cewa kan daliban Kano?

Abba Kabir ya dauki nauyi dalibai 1001 zuwa kasashen wajen wanda a yau Juma’a kason farko za su fara tashi su 550 zuwa Indiya.

Gwamna ya ce ya bi sahun mai gidansa ne Sanata Rabiu Kwankwaso wanda shi ne ya kirkiro shirin a lokacin mulkinsa a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida Ya Sake Daukar Nauyin Dalibai 1001 Zuwa Kasashen Duniya, Kwankwaso Ya Yi Martani

Gwamna ya shawarci wandanda su ka samu wannan dama da su zama mutane nagari wurin saka gwamnatin jihar alfahari da su yayin karatunsu.

Amartaninshi, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yabawa gwamnatin jihar kan bin tsarin da ya kirkiro da daukar nauyin dalibai zuwa kasashen waje.

Shi ma ya shawarci matasan da su yi duk mai yiyuwa don ganin sun amfani al’ummar jihar Kano da kuma kasa baki daya.

Gwamna Abba Kabir ya dauki nauyin karatun dalibai zuwa Indiya

Awani labarin, Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da shirin daukar nauyin dalibai zuwa kasashen waje.

Gwamnan ya ci gaba da tsarin Kwankwaso inda ya ware dalibai 1001 don daukar nauyinsu zuwa Indiya da Uganda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.